ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani and Sulaiman
2 months ago
Maulidin

A yayin zaman Maulidin Annabi Muhammad SAW da ke gudana duk shekara a zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Kaduna, karkashin jagorancin Shehu Isma’ila Umar Almaddah (Mai Diwani), ya yi kira ga masana, farfesoshi da kwararru masu kokarin kai sakon Annabi Muhammad SAW da su fahimci cewa, Addinin Annabi na duk duniya ne ba ga Hausawa kadai ba.

Zaman na wannan shekarar, ya gudana ne daga daren Litinin zuwa wayewar garin Talata, 25 ga watan Agustan 2026.

Bayan Isti’aza da basmala da salatin Annabi Muhammad SAW, Mai Diwani ya fara da godiya ga Allah, da ya kara dawo mana da wannan dare na haihuwar mafificin halitta, masoyin halitta, Annabi Muhammad SAW, masoyin Ubangijin halitta. Da muke dada godiya wa Allah, muke raya daren haihuwan nasa, kamar yadda idan Ramadan ya zo, muke raya shi da Kur’ani, da tafsirin Kur’ani, da karanta Kur’ani. Ba cewa bama karanta Kur’ani ko bama tafsirin Kur’ani ba, sai a Ramadana. Amma kuma Ramadana ne ka kawo Kur’ani, ma’ana sabida a wannan lokacin ya sauka, to a wannan lokacin ake baje kolin sa.

ADVERTISEMENT

To don haka, wannan wata na Rabi’ul-Awwal, watan haihuwar Manzon Allah SAW, da muke tuna tawa kanmu wannan ni’ima da Allah tabaraka wa ta’ala ya yi mana, ta aiko rahama ga halitta, duk gaba daya, cikamakon Annabta, littafin sa cikamakon littafai da falololi da basu da adadi. Ya aiko shi don ya cika kyawawan halaye SAW.

To wai ba sai a wannan wata muke raya maulidin Manzon Allah ko haihuwar Manzon Allah ko tarihin Manzon Allah ko labarin Manzon Allah ba, amma wannan watan, lokacin baje kolin sa ne, sabida a wannan lokacin ya sauka. Kowanne abu, akwai lokacin sa.

LABARAI MASU NASABA

Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)

Kamar yadda na fada, wannan rana ce ta soyayya. Allah tabaraka wa ta’ala ya fadi falalar wadanda suke son Annabinsa, Annabi Muhammad SAW. Ya fadi narkon azaba da ya tanada wa wadanda basa son Annabinsa. To malaman mu sun ce wannan soyayyar da Allah ya fada, irin soyayyar nan ce da hankalin ka zai iya baka ita, tunanin ka da ganin abun zai iya baka ita.

Alal misali, yanzu, idan ka ga wani dan kwallo ya yi kokari, sai kaji kana son sa, ba wai don ko gidan ku daya ba, ko addinin ku daya, a’a sabida gwarzon namiji ne a wajen kwallo. Idan wani dan wasan kwaikwayo ya yi kokari sai kaji kana son sa, yanzu. A wannan lokacin, ka so shi saboda gwarzon namiji ne. Idan wani soja ya yi rawar gani, idan wani shugaba ya taka rawar gani, idan wani malami ya yi rawar gani, idan wani mai kudi ya yi rawar gani, ko waye, kuma wannan ba wai sai dan yaren ka ba, ba sai dan addinin ka ba, ba sai kaza ba, za ka ji kana son sa. Sunan wannan soyayyar, soyayyar gwarzon namiji. Wannan hankalin ka ne ya ba ka, karatun ka ne ya ba ka, karatun ta nutsu da kai ka ga ya dace ka so shi.

Toh akwai kuma soyayya ta can ciki. Soyayyar zuciya. Wanda muke wa iyayen mu, wanda muke wa ‘ya’yan mu, wanda muke wa annabin mu, da muke wa ubangijin mu. Toh wannan za ka ga, ita ba sai wai ka ga wani abu ba, ba sai ka ji abu ba, ita ce kuma babba. Amma waccan soyayya ta hankali da ta ilimin nan, ita za ta kai ka, ka zama kana da zurfi a cikin wannan. Toh duk mai son ya ji gwarzon namiji, duk mai son ya ji wani mutum mai kokari da ya ci nasara, a cikin al’ummar sa, ya ci nasara akan wani abu sabo da ya zo da shi. Wani irin mai hakuri, wani mai juriya, wani mai tausayi, wani mai kyakkyawan hali. In dai ya ji labarin Annabi Muhammad SAW, na gaskiya, toh zai so Annabi!

Toh, don haka, mun gode Allah a nan wajen. A irin wannan soyayyar ta gwarzon namiji, turawa ne ma suka rubuta cewa Annabi shi ne na farko, ya iya gyara al’umma. Ya iya gyara har an samu wanda yake cewa, da Allah zai sa Annabi Muhammad ya dawo wannan lokacin. Kofi guda daya kawai zai ajiye a gaban sa, zai gyara duk wannan abu da ake yi, duk gabaki daya. Irin yanda ya gyara wancan lokacin. Toh ka ga yanzu wannan soyayya, ba wai soyayya ce ta addini ba, a’a, soyayya ce ta hankalin sa da gaskiyar sa, da amanar sa ta bashi.

Allah ya ce ba za mu iya daidaita soyayyar matan mu ba, ko ‘ya’yan mu, ko, ba za mu ce son da muke yi wa wancan za mu yi wa wancan ba. Saboda wannan abu ne a zuciya Allah yake sa shi. Amma kuma duk wanda ya yi kokari, zaka iya son sa. Toh in kuma ka ga mutum ya yi kokari ka ji ba ka son sa yanzu kuma abun ya zama hassada. Ya zama kuma ba gaskiya kake so, toh dan haka, a nan ne za ka ji an ce za a yi wa wanda bai san Annabi azaba, sabida ya karanta ya ga gwarzon namiji, ya ga abu. Maimakon ya yi ma irin wannan soyayyar da yake wa dukkan wani wanda ya shahara, toh shi kuma sai abun ya kai masa hassada. Amma soyayya kuma ta can ciki, soyayya kuma mai zurfi, soyayya zuciya, wacce ake kira da Wuddu, wannan baiwa ce ta Allah. Allah ba zai kama dan Adam da abin da ba shi da karfi a kan sa ba, duk gabaki daya.

Toh mun gode Allah, akan wannan muke taruwa, mu gaya wa duniya, ba wai iya mu musulmi ba, ba wai iya mu ‘yan Afirka ba, ba wai iya larabawa ba. A’a, duk duniya muke gaya mata, rahamar manzon Allah, SAW.

Toh, dan haka, a nan nake kiran malaman mu, nake kiran duk sauran kwararru, farfesoshi, likitoci, wanda suke so su kai sakon Manzon Allah SAW, su kula da cewa Annabi Muhammad, Annabin halitta ne. Ba wai suna kai sako ne ga mutanen mu Hausawa kadai ba, suna kai sako ne ba ga Hausawa kadai ba, sakon Annabi na kowa ne – Turawa, Chanawa, Jamusawa, Rashawa, da sauransu. Dan haka, in dai gaskiya za ka fada, ba za ka ji ta’addanci a addinin sa ba, sabida shi rahamane ga halitta, kuma rahamane ga mabiyan sa, “bil mu’minina ra’ufun rahimun”, SAW.

To dan haka mu gyara addinin mu, mu gyara karatun mu, mu gyara makarantun mu, mu bi wayewa. Manzon Allah SAW, shine cikamakon annabawa. Annabawan nan sune karshen malinta, sune karshen wayewa. Sune malaman addini a manzanci, kuma sune malaman kimiyya da fasaha a annabci.

Annabi Nuhu AS, yayi kira zuwa ga bautan Allah, da girmama iyaye, da a so ‘ya’ya, amma ya kera jirgin ruwa kuma ya tsiratar da halitta a yana injiniya, nan kuma a annabta, yayi wannan. Haka Annabi Salihu yayi kira a yana manzo, ya fito da rakumi kuma a yana annabi, haka Annabi Ibrahim AS, yayi kira a yana ma’aikin, ya gina mana wannan dakin Allah (Ka’aba), a kuma yana ma’aikin, a manzo. Sabida haka, an rawaito cewa Manzon Allah SAW, Annabi Muhammad, in yana zaune a gida ba wani abu yake ba, sai yace ku kawo kayan ku wanda yayi yage, in dinke muku.

Annabi Muhammad SAW, shi ne wanda ya tsara mulkin Larabawa din nan, ya tsara daular musulunci din nan, ya tsara wayewar su, ya tsara koman su, wanda har abada, in dai ba wanda suka gocewa karatun sa ba, ba wanda zai ce Annabi SAW, kauyanci ya kawo wa halitta, ko ci baya ya kawo mata, ko jahilci.

Dan haka, don Allah, mu tsamo addinin Annabi, mu tsamo karatukan Annabi SAW, daga zancen bidi’a ko zancen sunna, ko zancen alwala, ko zancen kaza da kaza, annabin da yaje har al’arshi, da yaje sama, da saman sama, kuma abunda zai nuna mana gaskiya ya je, gashi mu ma yanzu, Turawa da Chanawa suna zuwa, a 1969, sun yi combo a Apollo 11, sun je duniyar wata. Kaga ashe annabin mu gaskiya ne, yaje.

Annabin mu da ya yi tafiya daga Makka, zuwa Baitul Makdis a dan wani lokaci na dare, akan wani abu mai suna Buraka, Isra’i da muke cewa, abunda zai nuna mana gaskiya ne Annabi yayi, yanzu gashi nan muna ta tafiye-tafiye a jiragen sama, kuma cikin kankanin lokaci, an isa wurin nufi. Kaga ashe lallai Annabi ya hau Buraka, to hawan sa Buraka din nan ya nuna duniya za’a iya hawan jirgin sama. Zuwan sa al’arshi, ya nuna acikin duniya din nan za’a iya zuwa duniyar wata, gashi nan ana harba roket a je, har yau ba’a isa wani tauraron ba, sai dai kemara ce ta isa, sai dai inji ne ya isa, amma har yau dan’adam bai isa ba, har yau Kur’ani yana cewa ku matso dai, ku matso dai, ku matso dai, to mu rike karatun duniya din da na lahira din duk gabaki daya, Annabi SAW, ba wani mutum ne da yake zaune a masallaci kawai da katon gemu da asuwaki a baki da kaza da kaza ba, a’a, kwararre ne, hatta gine-ginen Madina, shi ya shirya su, SAW.

A fagen daga komanda ne, yasan ga inda za’a tsaya, ga inda za’a yi kaza, shine mai tsaro, kwana yake sallah, duk abunda zai faru a kunnan sa. Wata rana an ji kara a Madina, Sahabbai suka dinga taruwa, sai da suka taru, sannan suka nufi wurin, sai ga Annabi har ya dawo shi akan dokin Abu Dalha, shi har yaje ya gano meye, ya dawo. Annabi yace kar ku ji tsoro, “latura’u”, kar ku ji tsoro, an isan muku ko meye.

To mun gode Allah. Annabin mu, Annabin soyayya ne, mu so soyayya tsakanin mu. Duk mu musulmi da duk al’umma, abunda zai hada mu yafi yawa akan abunda zai raba mu. Kowa ya rike fahimtar sa, amma akwai fahimta kuma ta gaba daya, wanda duk zamu iya tafiya akan ta a zaman lafiya da komai, Allah ya bawa kasar mu lafiya, da zaman lafiya.

Mu rike addu’a kuma mu rike ‘yancin mu, mu zabi wanda muke ganin za su sa kasar mu ta ci gaba, da ‘yan ƙasar mu, wayayyu kwararru wadanda suka karanci siyasan nan, suka karanci mulkin nan, suka karanci abun nan, ba cewa kabila ta, ko addini ba. Sabida yanzu in kaje asibiti zaka ce ina likita musulmi? Sai da kace ina likita kwararre! In an ce ma irin wannan rashin lafiyar ma, ba kwararre a nan sai Ingila, kwashe kayan ka zaka yi ka tafi Ingila.

Mun gode Allah, Shugaban mu Sheikh Ibrahim Inyass RA, ya na daga cikin wanda ya fara wayar da kan malamai da manya, su tafi irin wadannan kasashe. Da yawa ya je ya kwanta asibitin Faransa, da Allah yayi karshen rayuwa ma a Ingila ya rasu.

To don Allah mu waye, mu zabi kwararru, ba ma kin kowa, muna son kowa, duk dan Nijeriya yana da ‘yancin ya mulki Nijeriya, ko waye. Haka Sheikh Ibrahim yace: “Al’ifrikiya lil’ifrikiyin,” Afirka ta ‘yan Afirka ce, kuma ko waye. Haka shehu ya gayawa turawan mulkin mallaka, yayi littafi akan wannan, wannan littafi an fassara shi da yaruka daban-daban: Faransanci, Italiyanci, yaren mu na Afirka, an fassara wannan littafi wajen ashirin da wani abu, sabida muhimmancin sa, Shehu yace Afirka ta ‘yan Afirka ce. Kuma koma waye in dai dan Afirka ne, in dai kwararre ne. Muna so ya rike mana Afirka ta cigaba, haka mu ma Nijeriya ta ‘yan Nijeriya ce, ko waye.

wAllah ya sa mu yi zabe lafiya, mu zabi alheri, abunda zai ciyar da kasar mu, ya ciyar da ‘yan kasar mu gaba, duk gabaki ɗaya. Mu bar kabilanci, mu bar kwadayi, mu bar hassada, mu bude idon mu, mu waye, don kasar mu ta cigaba, ya zama muna da kere-kere, ya zama muke kere-keren kayayyakin mu, mu muke noman mu, mu muke koman mu duk gabaki daya, duk muna da wannan abubuwa. Allah ya bamu wanda zai rike hannun mu ya zuwa cigaba, Alhamdulillahi.

Maulidin
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ posts Bio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)
Maulidin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair
  • Sulaiman
    Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

MASU ALAKA

SAW
Dausayin Musulunci

Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

October 16, 2026
SAW
Dausayin Musulunci

Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (2)

October 2, 2026
SAW
Dausayin Musulunci

Rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) Da Abin Da Ya Ta’allaka Da Aurensa (1)

September 25, 2026
Next Post
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

Zancen Tsige Wani Malami Don Ya Yi Kamfen Wa Tinubu Wasan Kwaikwayo Ne – Sheikh Disina

October 23, 2026
Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

Ɗan Obasanjo Ya Shiga Tafiyar Ƙungiyar ‘Tinubu Must Stay Movement’

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.