Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh. Ƴan uwa masu karatu da ke biye da mu a wannan shafi mai albarka ina muku barka da Juma’atu babbar rana. Mako biyu da suka gabata, darasinmu yana magana ne a kan fasaha da balagar harshen Manzon Allah (SAW).
To, a wannan makon za mu ɗora da darasi a kan hikimomin kalaman Manzon Allah (SAW).
Haƙiƙa an tattaro daga kalmominsa (SAW) wanda babu wani kafin shi da ya taɓa faɗa na hikimomi a cikin duk ƙabilun Larabawa da waɗanda ba su ba, shi ya fara faɗar su. Babu wani ɗaya daga cikin masu Hikima da za a auna shi da Annabi (SAW).
Yana daga cikin Hikimomin da shi ya fara faɗarsu:
Hamiyar waɗisu – Tanderu sun yi zafi; Annabi (SAW) ya faɗa wannan a ranar yaƙin Hunaini, yaƙi ya yi yaƙi, Sahabbai ba dama su gudu su bar Addininsu da Annabinsu, ta ɓangaren Kafirai su ma sun fito da duk rayuwarsu ba dama su gudu su bar iyalansu, kowa babu damar gudu, yaƙi ya yi yaƙi, da Annabi (SAW) yaga irin yadda idon kowa ya rufe ana ta gwabza yaƙi sai ya ce “Hamiyar waɗisu – Tanderu sun yi zafi”.
Mata Hatfa Anfihi – Ya mutu dolensa; Ma’ana ya mutu a gida ko mutuwa irin wacce take zuwa ba tare da ana tsammaninta ba, ko a ce ya mutu cikin lafiya. Larabawa a Jahiliyya da farkon Musulunci ba su so su mutu a gida, an fahimci hakan ne a faɗin Sayyidina Umar ga Usman bin Maz’unu yayin da yake cewa “Ina ganin girman Usman bin Maz’unu sai da na ga ya mutu ba a wurin yaƙi ba, sai na ce ashe ma ba wani ba ne, har sai da na ga Annabi (SAW) Ya Mutu a gida sai na fahimci cewa mutuwar gida ba ita ke nuni da ragwanta ba”. Usman bin Maz’unu Baƙuraishe ne, Sufi mai yawan Ibada, shi ne wanda da ya mutu Annabi (SAW) ya yi shaida a ƙabarinsa yana cewa na yi shaida ne sabida in ƴan gidana sun mutu in bizne su kusa da shi.
La yuldagul Mumin fi Hujrin Marrataini – Ba a sarar Mumini a cikin rami ɗaya sau biyu; Ma’ana shi Mumini mai takatsantsan ne, idan ya shiga wani lamari ya ga abin bai yi kyau ba, ba zai ƙara shiga ba. In kuma ya ƙara shiga lamarin ya sake afkuwa to ya zama wawa.
Assa’idu man wu‘iza bigairihi – Mai arziƙi shi ne wanda ya gargaɗu da abin da ya samu waninsa; Ma’ana wanda yaga wani abu ya samu ɗan uwansa na daga bala’i to ya kamata shi ma ya san abin da ɗan uwansa ya aikata hakan ta faru da shi, shi ma sai ya kiyaye kafin abin shi ma ya zo kansa.
Irin waɗannan suna da yawa wanda mai karatu ba zai iya tattare su ba. Abin da mai duba zai riska su ne mamakai cikin abin da ta tattare su kuma hankali ya tattare ta na daga ƙarshenta.
Sahabbansa sun ce da shi (Annabi Muhammad SAW) Ya Rasulullahi ba mu ga wanda ya fi ka fasaha ba, sai Annabi ya ce “Me zai hana in zama na fi kowa fasaha? Da halshena aka saukar da Alƙur’ani” Ma’ana Alƙur’ani yarena ne. In Bahaushe bai yi Hikima cikin Larabci ba, ba komai duk da cewa Hausawan suna shiga cikin yaren su koya har su fi ƴan yaren ƙwarewa. Kusan duk masu Hadisai kyawawa guda shida ba Larabawa ba ne amma sun ƙware, Larabci yaren duk Musulmi ne.
Alhamdulillah, yanzu duk wannan karatun da ƴan Nijeriya suke yi na boko, da (a ce) da yarensu ake karantarwa, da yanzu sun fara ƙirƙire-ƙirƙire, amma dole sai sun fara iya yaren kafin su fara neman sanin ilimin Karatun.
Sannan kuma Annabi (SAW) ya sake faɗa a wani lokaci “Ana afsahul Arabi, baida anni min Ƙuraishin, wa nasha’atu fi bani Sa’adin – Ni ne mafi fasahar Larabawa, sai dai ni ɗan Ƙuraishawa ne, kuma na tashi a cikin Bani Sa’adin” wannan nau’in maganar yana nufin ƙarfafa yabo ta hanyar nau’in zargi.
Kamar misalin yabon wani malami ga Shehu Ibrahim Kaulaha yake cewa “Shehu Ibrahim, mutum ne mai kyauta, sai dai duk yawan abin da ya ba ka sai ya raina shi (wato shi Shehu ne zai rana abin ba wanda aka ba, ba.”
Don sabida kwaɗayin ƴaƴansu su koyi fasaha, Larabawan Birni suke bawa Larabawan Ƙauye ƴaƴansu su taso a ƙauye.
Annabi (SAW) sabida Baƙuraishe ne kuma ya taso a bani Sa’adu a ƙauye sai aka tara masa ƙarfin bara’uwar ƙauye. Yanzu mutumin ƙauye da ka faɗa masa Magana, zai dawo maka da wacce ta fi taka, har ka ji mutum yana cewa ko dai dama yana jira na ne in yi masa magana. Suna da karin magana da baƙar magana.
Kuma An haɗa masa da gogewar lafazin birni da adon maganganun ƴan birni sannan kuma ka haɗa da cewa Annabin Allah ne wanda madadinsa ke zuwa daga Allah, wanda Ɗan’adam bai iya kewayewa da iliminsa.
Ummu Ma’abadin ta faɗa cikin yadda ta siffanta Annabi (SAW) cewa Maganarsa tana da daɗi, a rarrabe yake yin magana, ba magana ƴar kaɗan wacce ba ta biya buƙata ba kuma ba azarɓaɓi ba (surutu, ba tsayawa, ba ma’ana), kai ka ce maganarsa tsakiya ce da aka tsara, don haka aka rubuta maganarsa a matsayin Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya kasance mai gwarjin murya amma mai daɗin murya.
Yanzu kuma bari mu juya akalar darasin namu zuwa abin da ya shafi ɗaukakar Danganensa da girman garinsa da wajen tasowarsa mai girma (SAW).














