Tsohon Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Ƙasa (NPA), Arch. Aminu Dabo, na shirin sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar ADC, inda ake sa ran zai ɗauki ragamar zama Babban Daraktan Kamfen ɗin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, a Jihar Kano yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027. Wata majiya ta kusa da Aminu Dabo ce ta tabbatar da wannan shiri a birnin Kano, tana mai bayyana cewa an kammala tsare-tsaren miƙa masa jagorancin fafutukar siyasar Atiku a jihar.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Aminu Dabo ya ajiye muƙaminsa na Shugaban Masu Ruwa da Tsaki (Caucus Chairman) na Jam’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Dambatta tare da fita daga jam’iyyar gaba ɗaya. A cikin wata wasiƙar murabus mai kwanan wata 7 ga watan Oktoba, 2026, da ya aike wa shugaban jam’iyyar na Mazabar Dambatta Gabas, Dabo ya bayyana cewa ya yanke shawarar ne bisa dalilai na kashin kai da kuma tsare-tsarensa na gaba, inda ya nuna godiya ga shugabancin jam’iyyar mai mulki bisa kyakkyawar alaƙar da suka yi aiki a kanta.
Bincike ya nuna cewa murabus ɗin Dabo ya biyo bayan fitar da jerin sunayen kwamitin gudanar da kamfen ɗin shugaban ƙasa da na gwamna na APC mai mambobi 16 a Jihar Kano, wanda Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha, Umar Haruna Doguwa ya sa wa hannu, inda aka cire sunan Aminu Dabo gaba ɗaya daga ciki. Kwamitin, wanda tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ke jagoranta, shi ne aka ɗora wa alhakin shirya dukkan harkokin kamfen ɗin APC na 2027 a jihar.
Da yake tabbatar da batun ficewarsa ta wayar tarho daga Abuja, Dabo ya bayyana cewa ya miƙa wasiƙarsa ga jami’an jam’iyya a matakin gunduma a hukumance.
Sai dai kuma, duk da cewa majiyoyi na kusa sun tabbatar da shirinsa na ɗaukar ragamar kamfen ɗin Atiku Abubakar a Jihar Kano, a hukumance Arch. Aminu Dabo ko kuma jam’iyyar ADC ba su riga sun fitar da sanarwar ayyana sauyin sheƙar ko naɗin nasa ba a daidai lokacin haɗa wannan rahoto.














