Yau 20 ga watan Satumba, aka bude taron masana’antun kere-kere na duniya na shekarar 2026 a Hefei na lardin Anhui. Wang Dongming, mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilan jama’a ta kasa, ya halarci bikin bude taron, kuma ya gabatar da jawabi.
Wang Dongming ya ce, masana’antun kere-kere su ne tushen tattalin arziki, kuma su ne tushen karfin kasa. Karkashin jagorancin sakon taya murna da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika zuwa taron masana’antun kere-kere na duniya na shekarar 2019, Sin da sauran kasashen duniya suna hadin gwiwa ta kut da kut, wajen habaka masana’antun ta hanyar hada fasaha ba tare da gurbatta muhalli ba, domin ba da gudummawa mai kyau wajen habaka masana’antu na duniya cikin inganci, da samun moriyar juna da nasara tare.
Taken taron shi ne “fasaha ta gina duniya da samar da kyakkyawar rayuwa”, inda baki sama da 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 50 na duniya suka halarta. (Amina Xu)














