Aƙalla mutane tara ne suka mutu a wasu hare-haren ƴan bindiga da aka kai a yankunan Barkin Ladi da Riyom, da wasu al’ummomin da ke maƙwabtaka da su a Jihar Filato, tsakanin daren Asabar da safiyar Lahadi, 20 ga Satumba, 2026.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai fasinjoji da ke kan hanyarsu ta zuwa Gana-Ropp da kuma wani fasto da ke hanyar zuwa coci.
Rahotanni sun ce mutane biyar ne aka kashe a Gana-Ropp da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi, bayan wasu mahara sun farmaki fasinjojin da ke tafiya a matsayin ma’aikata. Shugaban Ƙungiyar Ci gaban Mwaghavul (MDA), Bulus Dabit, ya tabbatar da kisan, yayin da shugaban matasan Pyem na Gana-Ropp, Ukasha Garaba, ya ce an kwashe gawarwakin mutum biyar daga wurin harin.
A wani harin daban da aka kai a Dorowa Babuje, Barkin Ladi, an kashe mutane biyu, ciki har da wani fasto, waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa coci a safiyar Lahadi. Haka kuma, an kashe wata mata a Baten Wereng, Ƙaramar Hukumar Riyom, a daren Asabar, 19 ga Satumba, yayin da aka kashe wani mutum a Ratyidi, da ke gundumar Fan.
Mai magana da yawun Ƙungiyar Berom Youth Moulders (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da hare-haren tare da yin Allah-wadai da kashe-kashen. Ya buƙaci jami’an tsaro su ƙara yawan jami’ai a yankunan da ke cikin haɗari domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. A halin da ake ciki kuma, an rawaito satar wasu shanu a Dorowa Maranba da yankin Kantoma da misalin ƙarfe 3 na dare, inda sakataren MACBAN na Barkin Ladi, Gambo Abubakar, ya tabbatar da rahoton satar tare da kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike.
Bulus Dabit ya yi kira ga hukumomi da su ƙarfafa tsaro a yankunan da hare-hare suka fi shafa, domin bai wa mazauna damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali. Ya ce hare-haren da ake ci gaba da kai wa na jefa al’umma cikin tsoro da fargaba, yana mai buƙatar a kamo waɗanda suka aikata laifukan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.













