Albarkacin kaddamar da taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO na shekarar nan ta 2026, wanda aka bude a ranar 1 ga watan nan na Satumba, a ranar 1 ga watan Satumban nan, jirgin sama na farko da ya fara nuna shirye-shirye masu taken “CMG Showcase‑SCO Special”, ya tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Bishkek, fadar mulkin kasar Kyrgyzstan, inda taron ya gudana.
Kafar CMG ta Sin da kamfanin jiragen sama na China Southern Airlines ne suka yi hadin gwiwar fara nuna shirye-shiryen.
Shirye-shiryen kusan 20 da aka tsara bisa harsuna 15 na kasashe membobin SCO, wato harshen Kyrgyzstan, da na Rasha, da Turancin Ingilishi, da harshen Kazakhtan da Larabci, na kunshe da fasahohi masu inganci, kuma matafiyan dake zirga-zirga tsakanin hanyoyin sama har 155, ta jiragen China Southern Airlines, za su rika nishadantuwa da shirye-shiryen yayin da suke a kan hanya.
Kazalika, akwai wasu shirye-shirye masu kayatarwa, daga manyan kafofin watsa shirye-shirye na kasashe membobin SCO, ciki har da kafar gidan talabijin da radio na Kyrgyzstan, da kamfanin gidan talabijin da radio na Rasha, da kafar watsa shirye-shirye ta jamhuriyar musulunci ta Iran.
Fasinjoji za su rika samun damar kallon abubuwa masu nasaba da tarihi, da al’adu, da harkokin al’ummun kasashen hadakar ta SCO ta jerin fina-finai da shirye-shiryen da aka tanada.
Za a ci gaba da nuna shirye-shirye masu inganci ta harsuna daban daban a cikin jiragen saman, tun daga yanzu har zuwa karshen shekarar nan ta 2026, ta yadda jiragen za su zamo dandalin samun nishadi daga harkokin musayar al’adu masu kayatarwa. (Saminu Alhassan)














