A yau Juma’a 6 ga watan Oktoba ne aka gudanar da taro karo na farko, kan kare lafiyar jama’ar Sin da kasashen Afirka a birnin Guangzhou. Inda cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta Sin, da cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta Afirka suka daddale da kuma sanar da “shawarar kafa sabon matakin dakile da kandagarkin cututtuka masu yaduwa tsakanin Sin da Afirka”.
Shawarar ta nuna cewa, har yanzu cututtuka masu yaduwa babban kalubale ne ga lafiyar al’ummar Sin da Afirka, wadanda ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, da kuma barazana ga lafiyar duniya.
Karfafa hadin gwiwar dakile da kandagarkin cututtuka masu yaduwa tsakanin Sin da Afirka, mataki ne na a zo a gani da ake dauka waje gina kyakkyawar makomar al’ummar Sin da Afirka bai daya a bangaren kiwon lafiya.
Ban da wannan kuma, shawarar ta gabatar da matakai guda bakwai, wadanda suka hada da zurfafa raba bayanai, da karfafa musayar fasaha, da habaka hanyoyin tuntuba, da ingiza samun ci gaba mai kyau, kana da horar da kwararru, da zurfafa hadin gwiwar mabambantan bangarori, har ma da dagewa kan samar da daidaito da moriyar juna. (Amina Xu)













