ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yansandan Sun Kama Mutane 244 Tare Da Ƙwato Bindigogi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

by Sadiq
1 week ago

Rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta ce ta kama mutane 244 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar a watan Agusta.

Kwamishinan ‘Yansandan jihar, Ibrahim Bakori ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano.

Bakori ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da mutane takwas da ake zargi da garkuwa da mutane, 28 da ake zargi da fashi da makami, bakwai da ake zargi da satar motoci, 19 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, 117 da ake zargi da faɗan daba da kuma wasu mutane 65 da ake zargi da aikata wasu manyan laifuka.

ADVERTISEMENT

Ya ce an gudanar da kamen ne ta hanyar amfani da bayanan sirri, samamen wuraren da ake zargin masu aikata laifuka na fakewa, sintiri na sa’o’i 24, binciken ababen hawa da mutane da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da shugabannin al’umma.

Kwamishinan ya ce jami’an rundunar sun kuma ƙwato ɗimbin miyagun ƙwayoyi a yayin samamen.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Daga cikin abubuwan da aka ƙwato akwai sachet 17,070 da kwalaye biyar na Tramadol, sachet 49, kwalaye uku da fakiti 18 na Diazepam, sachet 90 na Pregabalin, ƙwayoyin Exol guda 210 da kuma tabar wiwi guda 614.

Bakori ya kuma ce rundunar ta ƙwato bindigogi ƙirar pistol guda uku da harsasai guda 65 da aka su dangantawa da safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ce an kuma ƙwato motoci guda shida, babura masu kafa uku guda huɗu da kuma babura guda bakwai da ake zargin ƙungiyoyin masu aikata laifuka sun mallaka ko suka yi amfani da su.

A cewarsa, ayyukan rundunar sun taimaka wajen rage manyan laifuka tare da inganta tsaro a wasu yankunan birnin Kano da a baya ake kallonsu a matsayin wuraren da ake yawan samun matsalar tsaro.

Ya bayyana Dala, Kofar Nassarawa, Sheka, Dorayi, Rimin Kebbe da Hotoro a matsayin wasu daga cikin wuraren da aka samu ingantaccen tsaro.

Sai dai Bakori ya ce rundunar na ƙara tsaurara ayyukanta a Bachirawa, Gobirawa da Tudun Fulani domin kawo ƙarshen ragowar ƙungiyoyin daba da ke ci gaba da aiki a yankunan.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da bai wa ‘yansanda sahihan bayanai kan ayyukan masu aikata laifuka a cikin yankunansu.

Kwamishinan ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Bakori ya kuma bayyana cewa rundunar ta fara shirye-shiryen tsaro domin tunkarar gangamin siyasa da babban zaɓen shekarar 2027.

Ya gargaɗi ‘yan siyasa da magoya bayansu da su guji kalaman ƙiyayya, tashin hankali da daba, yana mai cewa rundunar ba za ta bari irin waɗannan ayyuka su kawo cikas ga zaman lafiya a jihar ba.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
APC: Kotu Ta Soke Zaɓen Fidda Gwanin Sanatan Zamfara ta Arewa

APC: Kotu Ta Soke Zaɓen Fidda Gwanin Sanatan Zamfara ta Arewa

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.