Ma’aikatar kula da ma’aikata da al’umma ta kasar Sin, ta amince da tawagar kasar da za ta halarci gasar nuna kwarewa ta duniya ta 48. Tawagar ta kunshi mutane 220, da suka hada da masu fafatawa 71 da za su shiga dukkan gasanni 64.
Wadanda za su fafatan sun fito ne daga larduna 21, cikinsu har da dalibai 49 da ma’aikata 22. Kuma suna da matsakaicin shekaru 21, inda mafi kankantar shekaru shi ne 18 yayin da mafi girma ya kasance shekaru 25.Tun bayan fara shiga gasar a shekarar 2010, kasar Sin ta fafata cikin gasanni 7, inda ta samu lambobin zinare 93 da na azurfa 41 da na tagulla 28, da kuma lambobin karramawa ta hazaka 71.
Ita ce ke da mafi yawan lambobin zinare, kuma mafi yawan maki a gasanni 4 a jere.Za a gudanar da gasar ta 48 a birnin Shanghai na kasar Sin daga ranar 22 zuwa 27 ga watan Satumban bana, inda kimanin mahalarta 1,400 daga kasashe da yankuna kusan 70 za su fafata a kan dandali guda.
Gasar ta bana za ta zamo karo na 8 da Sin za ta fafata cikin gasar rukuni, kana karo na 3 da za ta fafata cikin dukkanin gasannin da za a yi. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)














