ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kama Na Hannun Daman Ganduje Kan Badaƙalar ‘Dala Dry Port’ A Kano

by Sadiq
7 months ago
Ganduje

An kama Ahmad Rabiu, tsohon kwamishinan ciniki na Jihar Kano kuma tsohon daraktan tashar Dala Inland Dry Port, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano yayin da yake shirin tashi zuwa Abuja.

Shi ne shaidar farko a shari’ar da ake yi wa Abdullahi Ganduje da wasu kan batun mallakar tashar.

  • Yadda Tayar Jirgin Sama Ta Ɓalle Bayan Tashinsa A Amurka
  • Da Pan Ji: Abincin Sinawa Da Na Fi So

Gwamnatin Kano ta ce Ganduje da abokan aikinsa sun canza hannun jarin jihar a tashar zuwa wani kamfani ba bisa ƙa’ida ba, inda aka karkatar da sama da Naira biliyan 4.49 da aka tanada don ayyukan tashar.

ADVERTISEMENT

Akwai ‘ya’yan Ganduje da ake zargi da zama daraktoci da masu hannun jari, kuma gwamnati ta ce an yi wannan canjin ba tare da bin doka ba.

Hadiminsa ya ce an kama shi ne yayin da yake shirin zuwa Abuja.

LABARAI MASU NASABA

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suna fuskantar laifuka 10, ciki har da karkatar da kuɗaɗen jama’a, cin amana da saɓa dokar mallakar dukiya.

Masu kare su sun ƙalubalanci wasu matakan kotu, bayan yin zama a bayan kan tuhume-tuhumen an ɗage shari’ar zuwa 23 ga watan Fabrairu don sauraron hujjoji na farko.

Masu gabatar da ƙara sun ce waɗanda ake tuhuma sun matsa wa wasu jami’an gwamnati da su rattaba hannu kan takardun da suka canza hannun jarin jihar na kashi 20 zuwa wani kamfani mai suna City Green Enterprise.

Sun ƙara da cewa kuɗaɗen da aka tanada don ayyukan tashar kamar hanyoyi, wutar lantarki, da katanga an yi amfani da su ne don amfanin ƙashin kai.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an yi canjin ne ba bisa doka ba, kuma ta gargaɗi jami’an gwamnati kan yin amfani da muƙamansu don amfanin kansu ko na iyalansu a kan kuɗaɗen jama’a.

Ana ci gaba da bincike, kuma ana sa ran samun ƙarin wasu shaidu za su bayar da shaida a makonni masu zuwa.

MASU ALAKA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Next Post
Kotu Ta Ware Kwanaki 10 Don Kammala Shari’ar EFCC Da Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele

Kotu Ta Ware Kwanaki 10 Don Kammala Shari’ar EFCC Da Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.