Wata kotu a Kano ta bayar da umarnin tsare wani mai amfani da kafar TikTok, Rabi’u Sani Zage, bisa zargin ɓata sunan jami’an Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA).
Ana tuhumarsa da laifuka guda takwas da suka shafi yin bidiyon jami’an KAROTA yayin da suke bakin aiki tare da wallafa su a kafafen sada zumunta, da wasu kalamai da ake zargin an yi su ne domin ɓata musu suna.
Hukumar KAROTA ta ce an taɓa kama wanda ake zargin a baya tare da gargaɗin sa da ya daina amma ya ci gaba.
Rabi’u Sani Zage ya amsa laifuka takwas da ake zargin sa da su a gaban Mai Shari’a Halima Wali ta Kotun Majistare mai lamba 7 da ke Nomansland, Kano.
Kotun ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali, tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba, 2026, domin yanke hukunci.
Haka kuma, kotun ta ajiye batun bayar da belinsa da lauyansa ya gabatar domin yanke hukunci a kai.














