ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, October 31, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sheikh Masussuka: Malaman Zaria Sun Bukaci Jami’an Tsaro Su Cafko Wadanda Suka Aikata Laifin

by Bello Hamza
1 hour ago

Malaman addinin Musulunci a birnin Zariya, Jihar Kaduna, sun yi kira ga hukumomin tsaro da su kara zurfafa bincike kan kisan gillar da aka yi wa marigayi Sheikh Masussuka, tare da tabbatar da gano wadanda suka aikata laifin da kuma hukunta su bisa doka.

An kashe Sheikh Masussuka ne a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba, 2026, lamarin da ya janyo damuwa a tsakanin malaman addinin Musulunci da sauran al’ummar musulmi.

Malaman sun kuma bukaci hukumomin tsaro da su yi amfani da sabbin dabarun bincike na zamani, tare da karfafa matakan tsaro domin hana sake aukuwar hare-hare kan malaman addini da sauran manyan mutane a cikin al’umma.

ADVERTISEMENT

Da yake magana kan lamarin, Sheikh Umar Sambo, Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Dogo Samaru, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake ci gaba da kashe fitattun malaman addinin Musulunci, ba tare da daukar kwararan matakan kamo wadanda ke aikata irin wadannan laifuka ba.

Ya koka da cewa kashe malaman addini na kara zama abin damuwa, inda ya jaddada cewa wajibi ne jami’an tsaro su wuce matakin rubuta rahotannin faruwar irin wadannan al’amura, su tabbatar da gano wadanda ke da hannu tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

“Wadannan ba su ne karo na farko ko na biyu da ake kashe fitattun malaman addinin Musulunci ba, amma har yanzu ba mu ga an dauki kwararan matakan kamo wadanda ke aikata wadannan laifuka da gurfanar da su a gaban shari’a ba.

“Lokaci ya yi da za a daina danganta irin wadannan hare-hare da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, ba tare da an yi kokarin gano su ba. Ya kamata jami’an tsaro su yi amfani da dukkanin fasahohin zamani da hanyoyin bincike da suke da su domin tabbatar da cafko wadanda suka aikata laifin,” in ji shi.

A nasa bangaren, wani malamin addinin Musulunci a Zariya, Alaramma Lukman Alfa, ya yi kira da a rungumi hakuri, juriya da zaman lafiya tsakanin musulmi, ba tare da la’akari da bambance-bambancen fahimtar addini da ke tsakaninsu ba.

Ya bayyana cewa babu wanda ya kamata a gallaza wa ko a kai masa hari saboda akidarsa ta addini, inda ya bukaci al’umma da su mutunta juna tare da warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa cikin lumana.

Ya ce, “Ya kamata mu rika hakuri da juna ba tare da la’akari da bambance-bambancen da ke tsakaninmu ba. Bai kamata a gallaza wa wani ko a kai masa hari saboda akidarsa ba.”

Sauran malaman da suka yi magana kan lamarin sun bayyana alhininsu bisa yadda rayuwar Sheikh Masussuka ta zo karshe, inda suka bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi.

Sun kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, su tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata laifin, tare da daukar matakan da suka dace domin kare rayukan malaman addini da sauran al’umma.

Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Yadda Masu Cutar Siga Za Su Rayu Cikin Aminci Da Irin Abincin Da Ya Dace Su Ci
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    2027: Gwamnonin Kano Da Kaduna Sun Yi Gargaɗi Kan Kalaman Ƙiyayya, Labaran Ƙarya
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Jihar Kano Za Ta Amfana Matuka Da Gidauniyar Aliko Dangote – Masu Ruwa Da Tsaki

MASU ALAKA

Cutar Ebola Ta Ɓulla A Nijeriya
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

October 31, 2026
NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000
Labarai

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

October 31, 2026
Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su
Labarai

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

October 31, 2026
Next Post
Tsarin Dimokuradiyya Mai Sauraron Al’umma Da Mika Shawararsu Ga Shugabanni, Basirar Sin Ce Wajen Neman Ra’ayoyin Jama’ar Kasar

Tsarin Dimokuradiyya Mai Sauraron Al'umma Da Mika Shawararsu Ga Shugabanni, Basirar Sin Ce Wajen Neman Ra’ayoyin Jama’ar Kasar

LABARAI MASU NASABA

Tsarin Dimokuradiyya Mai Sauraron Al’umma Da Mika Shawararsu Ga Shugabanni, Basirar Sin Ce Wajen Neman Ra’ayoyin Jama’ar Kasar

Tsarin Dimokuradiyya Mai Sauraron Al’umma Da Mika Shawararsu Ga Shugabanni, Basirar Sin Ce Wajen Neman Ra’ayoyin Jama’ar Kasar

October 31, 2026
’Yansanda Sun Tabbatar Da Kashe Sheikh Yahaya Masussuka Da Abokinsa A Katsina

Sheikh Masussuka: Malaman Zaria Sun Bukaci Jami’an Tsaro Su Cafko Wadanda Suka Aikata Laifin

October 31, 2026
Christine Lagarde: Yadda Kasar Sin Ta Samu Nasarar Rage Talauci Abin Burgewa Ne

Christine Lagarde: Yadda Kasar Sin Ta Samu Nasarar Rage Talauci Abin Burgewa Ne

October 31, 2026
Cutar Ebola Ta Ɓulla A Nijeriya

Da Ɗumi-ɗumi: An Gano Mutane 2 Da Ake Zargi Na Ɗauke Da Ebola A Arewa Maso Gabas – NCDC

October 31, 2026
NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

NLC Ta Matsawa Gwamnonin Jihohi Lamba Kan Tallafin Sufuri ₦70,000

October 31, 2026
Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

Ɗan Atiku Ya Yi Alƙawarin Ba Da Motoci 10 Don Yaƙin Zaɓen Tinubu

October 31, 2026
Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 6, Sun Kama Mutane 11 Da Ake Zargin Haɗin Kai Da Su

October 31, 2026
An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

An Kuɓutar Da Malaman Addinin Musulunci 3 Da Aka Sace A Zamfara

October 31, 2026
Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

Mutane 38 Sun Kamu Da Wata Sabuwar Cuta Da Ba A Gano Irinta Ba A Zamfara

October 31, 2026
Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

Peng Liyuan Ta Yi Hira Da Uwargidan Shugaban Kasar Jamus

October 31, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.