ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yanka Ta Tashi: Mai Neman Takarar Majalisar Dokokin Jiha A Tarauni Ya Musanta Janye Takara

by Abubakar Sulaiman
4 months ago

Ɗaya daga cikin masu neman takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tarauni, Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa), ya musanta ikirarin da Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ya yi na cewa ya janye masa takara bisa maslaha.

Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa) ya bayyana cewa har zuwa wannan lokaci bai janye daga takarar ba, kuma babu wanda ya tuntube shi domin tattaunawar maslaha ko neman ya hakura da kudirinsa na tsayawa takara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce labarin da aka yada na cewa ya janye wa Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ba gaskiya ba ne, yana mai cewa bai bayar da amincewarsa ga irin wannan matsaya ba.

ADVERTISEMENT

“Na ga sanarwar da Hon. Kabiru Dahiru Sule ADS ya fitar inda ya ambaci sunana cikin wadanda wai suka janye masa takara bisa maslaha. Ina sanar da al’ummar Tarauni cewa ban janye takara ba, kuma babu wanda ya tuntube ni ko ya yi wata tattaunawa da ni kan hakan,” in ji shi.

Ya kara da cewa yana nan daram cikin takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano domin wakiltar al’ummar Tarauni, yana mai jaddada cewa zai ci gaba da tuntubar al’umma da neman goyon bayansu.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Hon. Isa Adamu Bashir (Isa Jaa) ya kuma bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da ba shi goyon baya, yana mai cewa duk wani mataki da zai dauka zai kasance ne bisa gaskiya da mutunta ra’ayin jama’a.

Sai dai ya bayyana cewa yana girmama dukkan shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a siyasar Tarauni, tare da kira ga ‘yan siyasa da su rika tabbatar da sahihancin bayanan da suke fitarwa domin kaucewa rudani a tsakanin magoya baya.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su
  • Abubakar Sulaiman
    Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya
  • Abubakar Sulaiman
    Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso
  • Abubakar Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
Siyasa

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Next Post
Pantami Ya Fice Daga APC, Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna A PDP

Pantami Ya Fice Daga APC, Ya Samu Tikitin Takarar Gwamna A PDP

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Mutane 13 Da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

September 11, 2026
Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

Taron BRICS: Shettima Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Indiya

September 11, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

Gwamnan Shekara na 2026 Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang

September 11, 2026

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwarzon Gwamnan Shekarar 2026 Kwamared Nasir Idris

September 11, 2026

Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Janye Wa Atiku Ba A Zaɓen 2027 – Peter Obi

September 11, 2026
Farashin Siminti Zai Ragu Idan Farashin Kayan Aiki Ya Sauka – BUA

Gwarzon Shekarar 2026 Abdulsamad Rabiu

September 11, 2026
Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Buƙatar Ɗaukar Matakan Daƙile Yaɗuwar Cutar Mashaƙo A Nijeriya

September 11, 2026
Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

Ding Xuexiang Ya Halarci Taron Kolin CIFTIS Tare Da Ganawa Da Manyan Jami’an Kasashen Waje

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.