Jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar ton biliyan 2.35 na kayayyaki a watanni 7 na farkon bana, adadin da ya karu da kaso 0.7 a mizanin shekara-shekara, wanda ya samar da goyon baya mai inganci wajen rage tsadar jigilar kayayyaki da tabbatar da harkokin tattalin arziki na tafiya yadda ya kamata.
Matsakaicin abun da ake jigila a kowace rana ya tsaya kan taragon dakon kaya 187,000, adadin da ya karu da kaso 2.1 daga makamancin lokacin a bara. Bangaren sufurin jiragen kasa ya bayar da fifiko ga jigilar kayayyakin da ke da muhimmanci wajen raya tattalin arziki da rayuwar jama’a, wanda ke tabbatar da jigila cikin sauri da inganci. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
-
CGTN Hausahttps://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
ADVERTISEMENT