Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na matukar adawa da daukar bangare, da kafa rukunonin fito-na-fito dangane da fasahar AI.
Lin, ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka nemi ya yi tsokaci kan rahoton da ke cewa gwamnatin Amurka, na shirin aikewa da wata wasika ga sassan da suka sanya hannu kan sanarwar hadin gwiwa, dangane da damarmakin hadin kai a fannin fasahar AI, wadda za ta bukace su da su kauracewa zama membobin shirye-shirye biyu a lokaci guda.
Game da hakan, Lin ya ce, dukkanin kasashen na da ikon zabar kawancen hadin gwiwar da suka ga dama, bisa yanayin da suke ciki da kuma bukatunsu na ci gaba.
Jami’in ya kara da cewa, fatan shi ne dukkanin sassa masu nasaba, za su yi watsi da tunanin “na samu kowa ya rasa”, su mayar da hankali ga goyon bayan juna da cimma moriyar bai daya, da martaba ikon mulkin kai a harkar dijital na dukkanin kasashe, kana su yi aiki tare wajen ingiza nasarar managarcin tsarin jagorancin AI mai adalci da sanin ya kamata. (Saminu Alhassan)














