Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC (APC Presidential Campaign Council) ya caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, wanda kuma shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar ADC, bisa kiran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sunansa na yanka wato “Bola”, inda kwamitin ya bayyana hakan a matsayin rashin ladabi da wulaƙanta kujerar Shugaban Ƙasa.
Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen, Mista Dele Alake, shi ne ya fitar da sanarwar a madadin jam’iyyar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa matakin na Atiku babu dattaku da mutuncin da ake tsammani daga mutumin da ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa kuma a yanzu yake neman jagorantar ƙasar. Alake ya yi zargin cewa ƙiyayyar siyasa da ɗokin son mulki ne suka rufe wa Atiku ido har yake furta kalaman da ba su dace da gogaggen ɗan siyasa ba.
Kwamitin ya kalubalanci Atiku da cewa idan har yana ganin gwamnatin Tinubu ba ta tsinana komai ba, ya kamata ya fito da kwararan hujjoji, da tsare-tsare na bai ɗaya, da dabarun da za su gamsar da ƴan Nijeriya, maimakon mayar da martanin siyasa zuwa rashin kunya da rashin girmama gwamnati. Ya ƙara da cewa tsarin dimokuraɗiyya ya dace a gina shi a kan musayar ra’ayoyi da manufofi masu ma’ana ba wai zubar da mutuncin ofishin shugaban ƙasa ba.
Duk da wannan ɗabi’a da suka zarge shi da ita, sanarwar ta bayyana cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC ya umarci dukkan jiga-jigan jam’iyyar, da masu magana da yawunta, da magoya bayanta da su ci gaba da ba wa Alhaji Atiku Abubakar cikakkiyar girmamawa da ta dace da matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa, domin APC ta dogara ne a kan al’adun mutunta juna na gargajiyar Afirka.
A ƙarshe, Alake ya jaddada cewa yaƙin neman zaɓen Shugaba Tinubu na 2027 ba zai ɓata lokaci a kan musayar kalaman ɓatanci da abokan hamayya ba. Ya bayyana cewa za su mayar da hankali ne wajen tallata manufofin jam’iyya, da nasarorin da Shugaba Tinubu ya cimma a kan mulki, da kuma yadda sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake yi za su buɗe hanyoyin wadata da ci gaba ga al’ummar Nijeriya yayin da yake neman wa’adi na biyu.














