Asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Nijeriya ya kai dala biliyan 58.81 a ranar 12 ga Oktoba, 2026, matakin da ya kai matsayin da ba a gani ba cikin kusan shekaru 18. Ƙaruwar ta kai matakin da aka gani a baya ranar 19 ga Nuwamba, 2008, lokacin da asusun ya kai kusan dala biliyan 58.91, a cewar bayanan da CBN ya gabatar.
Alƙaluman Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa asusun ya ƙaru da dala biliyan 3.73 cikin kwanaki uku, daga dala biliyan 55.08 a ranar 9 ga Oktoba zuwa dala biliyan 58.81 a ranar 12 ga Oktoba. Tun daga ranar 1 ga Satumba, asusun ya ƙaru da dala biliyan 4.91, kwatankwacin kashi 9.1 cikin ɗari.
Wannan ci gaba ya zo ne bayan Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa asusun ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje bayan cire basussukan gajeren zango (net foreign reserves) ya kai dala biliyan 46, wanda ya ce sabon tarihi ne da aka kafa. Cardoso ya danganta farfaɗowar da ƙarin amincewar masu zuba jari da kuma matakan da ake ɗauka domin inganta kasuwar canjin kuɗaɗen waje.
Ƙaruwa a asusun ajiyar na iya ƙarfafa ƙarfin Nijeriya wajen biyan basussukan ƙasashen waje, da tallafa wa kasuwancin ƙasa da ƙasa da kuma rage matsin lamba kan darajar Naira. Haka kuma, tana iya ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwuiwa game da ƙarfin tattalin arziƙin Nijeriya.
Sai dai masana tattalin arziƙi sun jaddada cewa ɗorewar wannan ci gaba zai dogara ne da samun kuɗaɗen waje masu shigowa da zasu ɗore, da ingantaccen tsarin sarrafa basussuka da faɗaɗa fitar da kayayyakin Nijeriya zuwa ƙasashen waje.
A cewarsu, waɗannan matakai na da muhimmanci domin tabbatar da cewa ƙaruwar asusun ajiyar ta haifar da fa’ida mai ɗorewa ga tattalin arziki da rayuwar al’umma.














