Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Sokoto (SSU), ta bai wa Gwamnatin Jihar Sokoto wa’adin makonni biyu ta biya wa mambobinta kuɗaɗen alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin da ake bin su, ko kuma ta fuskanci yajin aiki.
Ƙungiyar ta bayar da wa’adin ne bayan wani taron majalisar ƙungiyar da aka gudanar ranar Talata, 8 ga Satumba 2026, domin duba matakin da aka ɗauka a taron ranar 24 ga Agusta da kuma tantance ƙoƙarin gwamnati wajen warware matsalolin rashin biyan haƙƙoƙin malamai.
A cikin wata sanarwa da Shugaban ASUU-SSU, Dr Bello Musa, da Sakataren ƙungiyar, Comrade Zulkallaini Shehu, suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce Ma’aikatar Ilimi Mai Zaman Kanta ta Jihar ta gana da ita ranar 7 ga Satumba.
Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin ganawar, gwamnati ta amince za ta magance buƙatun ƙungiyar cikin makonni biyu.Haka kuma, Ma’aikatar Ilimi Mai Zaman Kanta ta yi alƙawarin isar da buƙatun ƙungiyar ga Gwamnan Jihar Sokoto domin ɗaukar matakin da ya dace.
ASUU ta ce za ta sake duba matakin da za ta ɗauka bayan cikar wa’adin makonni biyu idan ba a biya haƙƙoƙin mambobinta ba.













