Albarkacin kewayowar bikin baje kolin kasa da kasa na Sin na shekarar 2026, na cinikayyar samar da hidimomi ko CIFTIS, kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar da binciken jin ra’ayoyin jama’a, wanda sakamakonsa ya nuna cewa, kaso 89.6 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu da yadda baje kolin ya bunkasa, zuwa muhimmin dandali na ingiza bude kofar kasar Sin bisa babban matsayi a fannin cinikayyar samar da hidimomi.
A karon farko, baje kolin CIFTIS na bana, zai tanadi yankin musamman na nune-nune “Hidimomin Sin”, don nuna sabbin nasarorin da kasar ta samu a fannin hidimomin dijital, da na al’adu, da tsarin aikewa da sakwanni na zamani da sauran sassa. Dangane da hakan, kaso 93.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun amince cewa, baje kolin CIFTIS ba kawai dandali ne na nune-nune ba, domin kuwa ya tanadi muhimmin dandalin cinikayya dake ingiza bude kofar babbar kasuwar Sin bisa babban matsayi.
A wani ci gaban kuma, a bangaren yankin nune-nune na “Hidimomin Sin”, kaso kusan 40 bisa dari na abubuwan da za a baje kolinsu na amfani da ne da muhimman fasahohin AI, da manyan harsunansa da sassan aiki masu basira. Har ila yau, a wannan karo za a gabatar da sabbin fasahohi, da hajoji wadanda za a nuna a karon farko ga duniya, ko aka fara nuna su a kasar Sin.
Kaso 90.3 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin sun gamsu cewa, sashen samar da hidimomi na kasar Sin na gaggauta bunkasa bangaren ingancin fasahohi, tare da fatan ganin cinikayyar hidimomin Sin, ta samar da yanayi na karin ingancin hidimomi masu aiki da fasahohi ga masu amfani da su na sassan duniya. (Saminu Alhassan)














