A yau Talata ne mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa Sin ta shirya sake daukar nauyin taron tattaunawa dangane da gina kwarewa a fannin fasahar AI, a jami’ar Peking dake nan birnin Beijing, tun daga ranar 7 zuwa 12 ga watan nan.
Jami’ar ta ce Sin za ta yi aiki tare da sassa daban daban, wajen mayar da fasahar AI wata damar cin gajiya mai dorewa, kana wani karfi da zai ingiza samar da walwala ga daukacin bil’adama.
Mao Ning, ta ce a wani bangare na ci gaba da kokarin aiwatar da tsarin aiki, na bunkasa kwarewa a fannin fasahar AI mai nagarta da game kowa, Sin ta kafa kawancen hadin gwiwar fasahar AI na duniya, a wani mataki na saukaka baiwa kowa da kowa damar cin gajiya daga fasahohi, da hidimomi masu nasaba da AI, tare da taimakawa kasashe masu tasowa samun damar bin tafarkin bunkasa fasahar AI mafi dacewa da bukatunsu.
Dangane da batun Taiwan kuwa, Mao ta ce yankin bai taba zama, kuma ba zai taba zama kasa ba. Ta ce jami’an gwamnatin Lai Ching-te na ta kokarin sauya gaskiya, dangane da kuduri mai lamba 2758 na babban zaman zauren MDD, wanda hakan ya kara fayyace aniyarsu ta a ware, da rajin neman “’Yancin kan Taiwan.” Sai da kuma, kalamai marasa ma’ana da suke furtawa ba za su taba sauya tarihi da dalilai na doka, dake tabbatar da matsayin bangarori biyu na zirin Taiwan, a matsayin kasar Sin daya tak ba, kana ba za su gurgunta tsaiwar sassan kasa da kasa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya ba.
Har ila yau, jami’ar ta ce kaso na hudu, na kayayyakin tallafin gaggawa da Sin ke aikawa kasar Nepal sun tashi da safiyar yau Talata. A cewarta, yayin da ake fuskantar bala’i mai muni, Sin za ta ci gaba da kasancewa tare da Nepal don ganin an shawo kan wahalhalun tare. (Saminu Alhassan)














