Daga Watan Janairu Zuwa Satumban Bana Harajin VAT Na Kayayyakin Sayayyar Daidai Da Sari A Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 4.4 Bisa Dari
Tun bayan shiga sabuwar shekarar nan ta 2026, maaikatar cinikayya ta kasar Sin ta aiwatar da kudurori yadda ya kamata, tare da gudanar da manufofin kwamitin kolin JKS da na majalisar zartarwar kasar, kana ta ingiza gina tsarin hada-hadar cinikayya na zamani, da yayata ci gaba bisa matsayin koli a fannin hada-hadar masanaantun sayayyar daidai da na sari. Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar a baya bayan nan, sun nuna yadda daga watan Janairu zuwa Satumban bana, yawan kudaden harajin VAT na masanaantun kasar a fannin sayayyar daidai da sari ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 11.1, adadin da ya karu da kaso 4.4 bisa dari a mizanin shekara-shekara, kana ya kai kaso 10.4 bisa dari na jimillar GDPn kasar. Kazalika, gaba daya ci gaban ayyukan masanaantun kasar yana kara bunkasa, tare da samar da tallafi mai karfi na fadadar bukatun cikin gida a dukkanin fannoni, da kuma karfafa hada-hadar hajoji a cikin gida. (Saminu Alhassan)



















