Xi Ya Gabatar Da Shawarwari 4 Na Bunkasa Hadin Gwiwar Hakar Ma’adinai Tsakanin Sin Da Afrika
Yau Talata da rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kasar Botswana Duma Gideon Boko, wanda ke ziyara a kasar Sin. Yayin tattaunawar da suka yi, Xi Jinping ya gabatar da wasu shawarwari 4 na bunkasa hadin gwiwar hakar ma’adinai tsakanin Sin da Botswana da ma Sin da Afrika. Da farko, ya ce ya kamata a daukaka ka’idar cewa albarkatun Afrika, mallakin Afrika ne. Kuma a shirye Sin take ta gabatar da gogewarta, tare da taimaka wa kasashen Afrika tsara shirye-shiryen bunkasa aikin hakar ma’adinai da suka dace da yanayin kasashen nahiyar. Na biyu, a rungumi ra’ayin hadin gwiwa mai daidaito da muradu na moriyar juna. Ya ce Sin za ta ci gaba da karfafa gwiwar kamfanoninta su bunkasa ayyukansu da kai fasahohi masu kare muhalli da suka dace da yanayin nahiyar da inganta hadin gwiwar kasashe masu tasowa a bangaren raya aikin hakar ma’adinai. Na uku, rungumar hanyar hadin gwiwa mai inganci. Ya ce Sin za ta ci gaba da ingiza sauye-sauye a hadin gwiwar hakar ma’adinai tsakaninta da Afrika, domin inganta ayyukan masana’antu da samar da sabbin dabarun samar da kudi masu araha da dorewa da goyon bayan tsarin zamanantar da Afrika ta hanyar hadin gwiwa mai inganci. Na hudu, daukaka muhallin hadin gwiwa mai adalci da bude kofa. Ya ce bai kamata albarkatun Afrika su zamo abun haifar da kiyayya tsakanin yankuna ba. Ya ce Sin tana maraba da kokari daga dukkan bangarori domin taimaka wa ci gaban nahiyar Afrika, kuma a shirye take ta hada hannu da bangaren Afrika din wajen samar da kyakkyawan yanayin da kamfanoni za su zuba jari da gudanar da ayyuka. A nasa bangare, Duma Gideon Boko ya ce a shirye Botswana take ta hada hannu kut da kut da Sin, da daukaka cudanyar bangarori daban-daban da karfafa hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa da inganta goyon baya da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika. Shugabannin biyu sun kuma sanar da daga darajar dangantakar kasashensu zuwa ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)



















