Sin Ta Bukaci A Mayar Da Hankali Kan Sauyin Yanayi Da Hadin Gwiwa A Babban Taron Arctic
Tsohon mataimakiyar ministan harkokin wajen Sin Fu Ying, ta yi kira ga kasa da kasa su kara hadin gwiwa kan binciken kimiyya da kare muhalli a yankin Arctic, tana cewa sauyin yanayi maimakon barazanar da kawai ake tunani, shi ne babban kalubalen da yankin ke fuskanta. Fu Ying ta bayyana haka ne lokacin da ta jagoranci tawagar Sin zuwa babban taron kasa da kasa kan yankin Arctic na 2026, wanda aka yi tsakanin Alhamis zuwa jiya Asabar a Reykjavik, babban birnin Iceland. Sama da wakilai 2,500 daga kasashe da yankuna 70 ne suka halarci taron domin tattaunawa kan batun da ya shafi fahimta da rayawa da ma shugabantar harkokin yankin Arctic. Yayin wani zaman da aka yi wa taken “Yadda za a fahimci kasar Sin,” Fu Ying ta tattauna da tsohon shugaban Iceland da shugaban taron yankin Arctic, Olafur Ragnar Grimsson. A cewarta, ainihin kalubalen da yankin Arctic ke fuskanta yanzu haka shi ne sauyin yanayi, kuma ya kamata kasashe su mayar da hankali da samar da albarkatu ga binciken kimiyya da kare muhalli, maimakon yin gasa kan barazanar tsaro da suke tunani ko hasashe. Da take tsokaci kan ci gaban Sin da rawar da take takawa a harkokin kasa da kasa, Fu Ying ta ce Sin na nacewa ga neman ci gaba cikin lumana, kuma ba ta neman yin babbakere a duniya, kuma ba ta yarda cewa duniya na bukatar wani sabon salon babakere ba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)



















