Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Tawagar Shugabanni Daga Kasashen Tsibiran Tekun Pacific
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da tawagar shugabannin siyasa daga kasashen tsibiran tekun Pacific, karkashin jagorancin mataimakin firaministan Tonga, Viliami Uasike Latu, a birnin Beijing yau Jumma’a. Wang ya bayyana cewa, bisa jagorancin hadin gwiwa na dukkan shugabannin kasashen da abin ya shafa, cikakkiyar alakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da kasashen tsibiran tekun Pacific ta kara zama babba wacce take gudana ba tare da tangarda ba. Wang ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen tsibiran tekun Pacific domin ba wa juna cikakken goyon baya wajen bin hanyoyin samun ci gaba da suka dace da yanayin kowace kasa kuma irin wadanda al'ummominsu suka zaba da kansu bisa cin gashin kai, da karfafa musaya da hadin gwiwa tsakanin jam'iyyun siyasa, da kuma hada hannu wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai-daya dake da kusanci sosai da juna a tsakanin kasar Sin da kasashen tsibiran tekun Pacific. A nasa bangare, Latu da sauran membobin tawagar sun gode wa kasar Sin saboda gagarumin taimakon da ta bayar a shekaru da dama ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na kasashen tsibiran tekun Pacific. Sun kuma ce kasashen tsibiran tekun Pacific za su kafe kai-da-fata wajen bin manufar kasar Sin daya tilo a duniya kuma a shirye suke su karfafa mu'amala da jam'iyyar JKS. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















