Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika sakon ta’aziyya ga Sarkin kasar Spain, Felipe VI a yau Alhamis, dangane da karon da jiragen kasa masu saurin gudu suka yi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane a lardin Toledo na kasar Spain.
A cikin sakon, Xi ya yi ta’aziyya sosai game da wadanda abin ya shafa, tare da nuna jimami na hakika ga iyalansu, a madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, bayan samun labarin cewa hatsarin ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Haka kuma, ya yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka ji raunuka a mummunan hatsarin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ADVERTISEMENT














