Sin Za Ta Bi Manufar Diflomasiyya Mai Zaman Lafiya Da Dogaro Da Kai
A bana ake cika shekaru 90 da cimma nasarar Doguwar Tafiya ta jar rundunar sojojin kasar Sin. Kuma a kwanan baya, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova, ta yaba da nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin neman bunkasa, inda ta bayyana kokarin da kasar Sin ta yi ta fuskar gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya, da kuma gudanar da shawarar Ziri daya da hanya daya cikin hadin gwiwa, a matsayin wata "Sabuwar Doguwar Tafiya". Dangane da wannan tsokaci, mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana cewa, babban ruhin "Doguwar Tafiya" ya zaburar da al'ummar kasar Sin, tare da karfafa musu gwiwar shawo kan matsaloli da kalubaloli, wanda hakan ya haifar da nasarorin kasar Sin a fannin neman ci gaba na a-zo-a-gani. A halin yanzu, da ake kan sabuwar "Doguwar Tafiya" zuwa ga farfadowar al'ummar kasar Sin, kasar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka, kan manufar diflomasiyya mai zaman lafiya da dogaro da kai, kana, za ta yi aiki tare da dukkan kasashe, ciki har da kasar Rasha, domin inganta zaman lafiya da ci gaban duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da su, wajen gina al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya. Haka kuma, yau Talata, wato ranar 20 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekara daya da kafuwar hukumar shiga tsakani ta duniya wato IOMed. Dangane da wannan batu, Mao Ning ta bayyana cewa, tun bayan kafuwarta shekara guda da ta gabata, hukumar ta samu goyon baya mai yawa, da kuma karbuwa daga kasashen duniya, inda adadin kasashen da suka shiga hukumar ya karu zuwa 48. Haka zalika, ta yi nasarar shiga tsakani wajen sasanta takaddamar kasuwanci ta kasa da kasa, lamarin da ya sa ta samu yabo matuka, daga bangarorin da abin ya shafa. (Mai Fassara: Maryam Yang)



















