Kasar Sin Na Tunkarar Ci Gaban Fasahar AI Yadda Ya Kamata
A zamanin nan da muke ciki zai yi wuya a tabo ci gaban duniya, ba a ambato irin tasiri da fasahar kirkirarriyar basira ko AI ke yi ga sassan rayuwar bil’adama ba. Fasahar AI ta zamo batun tattaunawa tsakanin masharhanta, inda wasu ke jinjinawa irin alfanu da take bayarwa ga ci gaban rayuwar bil’adama, da tattalin arziki, da taimakawa hidimomi, da binciken kimiyya da fasaha da sauransu, a daya bangaren kuma, wasu na ganin baiken fasahar bisa kallo da suke yi mata, na wadda ka iya illata moriyar bil’adama ciki har da kwace guraben ayyukan yi. Don game da hakan ne kuma, mahukuntan kasar Sin suka zabura wajen lalubo hanyoyin dakile duk wani mummunan tasiri da ake hasashen fasahar AI ka iya haifarwa ga jama’a. Alal misali, cikin manyan matakan da Sin ke dauka musamman a baya bayan nan, akwai batun aiwatar da wani shiri na bunkasa samar da guraben ayyukan yi domin tunkarar kalubalen hakan daga ci gaban AI. Karkashin wannan manufa, gwamnatin Sin na ingiza manufofin samar da guraben ayyukan yi ta yadda Sinawa za su ci gaba da cin gajiyar manufofi mafiya dacewa da zamanin yau. A cikin wannan shekara ta 2026 kadai, kasar ta fitar da jerin kundin bayanai masu kunshe da matakai daban daban wanda za a aiwatar don cimma nasarar more ci gaban fasahohi, ciki har da AI, tare da wanzar da guraben ayyukan yin jama’a tare. A cikin rahoton ayyukan gwamnatin kasar Sin na shekarar nan ta 2026 ma, gwamnatin kasar ta sha alwashin aiwatar da matakai masu tasiri na bunkasa samar da guraben ayyukan yi, da ciyar da sana’o’i gaba, ta hanyar yiwa fasahar AI kyakkyawan tanadi na kara shigar da ita harkokin jama’a. Har ila yau, karkashin wani shiri na shekaru biyar dangane da aiwatar da manufar “Ayyukan yi gaban komai”, an bayyana muhimmancin bunkasa cin gajiyar fasahar AI a matsayin daya daga muhimman ayyuka, tare da kira da a fadada samar da guraben ayyuka ta amfani da fasahohin AI, da ci gaba da cin gajiyar sassan ayyukan yi na gargajiya da aka saba da su. A halin da ake ciki, fasahar AI na ci gaba da sauya yanayin tattalin arzikin duniya, ciki har da na kasar Sin, tare da haifar da babban sauyi a kasuwar kwadago, inda ake ta ganin karin bukatar ma’aikata masu kwarewar gaske a fannin samar da hidimomin zamani. Wasu alkaluman baya bayan nan sun shaida cewa, jarin babban sashen fasahar AI na kasar Sin ya haura kudin kasar yuan tiriliyan 1.2, wato kusan dalar Amurka biliyan 178.23, kana sama da kamfanoni 6,200 na gudanar da hada-hada a fannin. Har ila yau, karin karbuwar fasahar AI a sassan manyan masana’antun kasar ya haura kaso 80 bisa dari. Ba a fannin fasahar AI kadai ba, kasar Sin tana kuma fatan fadada dabarun samar da guraben ayyukan yi ga ’yan kasar ta hanyar kyankyashe damarmaki daga masana’antu masu tasowa, da ma wadanda ake fatan za su kara yin tasiri a nan gaba. A bangaren AI, cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta shigar da sabbin fannoni 72 cikin jerin guraben ayyukan yi, ciki har da ayyana ma’aikata masu horaswa a fannin AI, da manajojin lura da yadda ake fitar da hayakin carbon, da hade su cikin tsarin jadawalin ayyukan yi na hukuma. Kuma tun daga farkon shekarar nan ta 2026, mahukuntan kasar sun sanar da karin wasu sabbin guraben ayyukan yi 11 a wannan fage. (Saminu Alhassan)



















