Nazarin CGTN: Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Nuna Kudurin Sin Na Bunkasa Bude Kofa
Yayin da ake gudanar da baje koli na 23 na Sin da ASEAN da taron bangarorin biyu kan kasuwanci da zuba jari, kafar CGTN ta gudanar da wani nazari tsakanin masu bayar da amsa a fadin duniya, inda kaso 90.9 suka yi imanin cewa, ci gaba da karbar bakuncin irin wannan baje koli, ya nuna tsayayyen kudurin Sin na bunkasa bude kofa. Baje kolin na wannan karo ya ja hankalin kamfanoni 3,300, inda ake sa ran masu sayayya 33,000 za su hallara. Cikin nazarin, kaso 89.5 na masu bayar da amsa sun ce baje kolin ba kawai muhimmiyar kafar nuna nasarorin hadin gwiwar Sin da kasashen ASEAN ba ne, wani dandali ne mai muhimmanci na bunkasa musayar kasuwanci da haduwar masana’antu da gabatar da damarmakin ci gaban yankin. An wallafa nazarin ne a dandamalin CGTN na harsunan Ingilishi da Sipaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 3950 suka kada kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

















