Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ƙaryata iƙirarin da ke cewa ya ba da umarnin kama wasu matasa, ciki har da magoya bayan jam’iyyun adawa ko masu sukar gwamnatinsa da ke sanye da rigunan da aka rubuta “Tinubu Must Go”.
Da yake magana a birnin Maiduguri, Gwamna Zulum ya bayyana mamakinsa kan yadda aka danganta gwamnatinsa da matakin da rundunar ƴansanda ta ɗauka na cafke wasu mutane a jihar kwanan nan, yana mai jaddada cewa shi kansa bai ma da masaniya kan kamen da aka yi ba.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai a halin yanzu shi ne tabbatar da zaman lafiya, da sake tsugunar da ƴan gudun hijira, da kuma sake gina ababen more rayuwa a Jihar Borno bayan shafe shekaru ana fama da rikicin Boko Haram, ba wai sa-in-sa da ƴan siyasa ba. Ya ce: “Ƴan siyasa masu neman suna ko waɗanda suka fidda rai ne kaɗai ke ba da umarnin kama magoya bayan adawa, kuma ni ba ɗaya daga cikinsu ba ne”.
Haka kuma, gwamnan ya jaddada cewa Jihar Borno ta na ƙarƙashin ikon jam’iyyar APC sama da shekaru goma, don haka ba shi da wata fargabar cewa jam’iyyun adawa za su iya samun nasara ta yadda zai buƙaci amfani da ƙarfin iko a kansu.
A ƙarshe, Farfesa Zulum ya bayyana cewa abu ne da aka saba gani a duk lokacin da babban zaɓe ke gabatowa, inda wasu ke ƙoƙarin ƙirƙiro zarge-zargen ƙarya a kan shugabanni domin neman jan hankalin al’umma a fagen siyasa.














