Babban bankin Sin, ko kuma bankin jama’ar kasar Sin wato PBC a takaice, ya gudanar da taron aiki na rabin karshen shekarar bana jiya Asabar, inda aka tabbatar cewa, bankin zai kara karfi a wasu fannoni kamar ci gaba da gudanar da matakan saukaka harkokin kudade, da inganta tattalin arziki na zahiri na ba da hidimomin hada-hadar kudi, da inganta gyare-gyaren tsarin shugabancin harkokin hada-hadar kudi na duniya, da kuma ci gaba da inganta matakin kulawa da ba da hidimomi na harkokin hada-hadar kudi.
Bugu da kari, game da zurfafa gyare-gyaren harkar kudi da bude kofa ga kasashen waje, bankin jama’ar Sin zai ci gaba da habaka gina tsarin biyan kudi da kudin Sin RMB a kasashen waje, da kara hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya wajen biyan kudi, da kuma inganta hanyoyi da abubuwan da suka shafi hada hadar kudin RMB ta dijital a kasashen waje.(Safiyah Ma)














