A jiya Laraba ne wani babban jami’in banki a kasar Africa ta kudu ya bayyana cewa, shirin shigo da kayayyaki daga nahiyar Africa ba tare da biyan harajin kwastam ba, da kasar Sin ta aiwatar, na matukar taimakawa harkokin kasuwanci a Africa, tare da rage kudaden da ake kashewa wajen fitar da kayayyaki, inda a gefe guda kuma hakan ke inganta tsarin mu’amalar cinikayya da kudin RMB tare da saukaka harkokin kasuwanci tsakanin Afrika da Sin.
Cikin wata sanarwar da ya fitar, Bill Blackie, babban jami’in harkokin kasuwanci da cinikayya na Standard Bank Group ya bayyana cewa, masu fitar da kaya daga Afrika zuwa kasashen waje, da suka hada da kasar Afrika ta kudu, da Kenya da Zimbabwe da kuma Najeriya, tuni suka fara ganin alfanun damar fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin kasar Sin, tun bayan aiwatar da tsarin Zero Tariff ga kasashen nahiyar Afrika 53, wanda aka fara tun a ranar 1 ga watan Mayun shekarar nan, da nufin karfafa alakar diflomasiyya tsakanin kasashen da kasar Sin.
Blackie ya kuma lura cewa, mu’amalar kasuwanci da kudin RMB na matukar taimakawa harkokin kasuwanci a kasashen, da kuma samar da damarmakin huldar cinikayya a kasuwanni, ta hanyar rage tarnaki wajen biyan kudi tare da bunkasa saukin mu’amalar kasuwanci tsakanin Afrika da Sin. (Suleiman Suleiman Ibrahim)














