Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC ya musanta zargin cewa ana shirin kashe tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC.
Kwamitin ya kuma musanta rahotannin cewa an janye jami’an tsaron da ke gadin Atiku, inda ya ce har yanzu ’yansanda da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) suna ba shi kariya.
A cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar ranar Talata, kakakin kwamitin, Dele Alake, ya bayyana zargin da tsohon kakakin APC, Timi Frank, ya yi a matsayin ƙarya, tare da ƙalubalantarsa da ya gabatar da hujjoji.
Kwamitin ya ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro ga ’yan takarar shugaban ƙasa da sauran muƙaman siyasa gabanin babban zaɓen 2027.
Ya buƙaci Frank da ya miƙa duk wata hujja da yake da ita kan barazanar tsaro ga hukumomin da abin ya shafa domin gudanar da bincike.
Sai dai, Frank ya nuna damuwa kan zargin shirin amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) wajen tsoratar da Atiku da kuma kama shi.
Ya kuma yi kira ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da sauran shugabannin ƙasashen duniya da su sa baki, tare da buƙatar gudanar da bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen.
A nata ɓangaren, kwamitin yaƙin neman zaɓen APC ya gargaɗi ’yan siyasa da su guji yaɗa zarge-zargen da ba su da hujjoji, waɗanda ka iya haddasa tashin hankali, tare da yin kira da a gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana da sanin ya kamata.














