ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, September 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babu Wata Sabuwar Ƙungiyar Ta’addanci a Kebbi — Kwamishina

by Sulaiman
2 months ago
Kebbi

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na Jihar Kebbi, Yakubu Ahmed, ya musanta rahotannin da ke cewa wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna “Sai Malam” ta bayyana a jihar.

Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar wata babbar tawagar kafafen yaɗa labarai domin kai ziyarar girmamawa ga Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin labarai na Nijeriya, Ali M. Ali, a Abuja ranar Talata.

Ya bayyana ikirarin a matsayin “ƙarya tsagwaronta” tare da cewa wani yunƙuri ne na yaɗa bayanan ƙarya domin rikita al’umma gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan ya kuma musanta wani rahoton kafafen yaɗa labarai da ya yi zargin cewa yara fiye da 130 ne ke mutuwa a kullum a jihar sakamakon yawan mace-macen yara, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, binciken da hukumomin tsaro suka gudanar ya nuna cewa ƙungiyar da ake kira “Sai Malam” ta ƙunshi wasu matasa da ke aikata laifukan yanar gizo da kuma damfarar mutane ta hanyar intanet.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Ya ce, “Lokacin da aka fitar da wannan bayanin, ya tayar da hankalin kusan kowa. Mun samu kira da yawa daga sassa daban-daban na ƙasar nan da ma ƙasashen waje suna neman tabbatar da sahihancin wannan labari.

“Abin da bincike ya gano shi ne cewa ba ƙungiyar ta’addanci ba ce, sai dai wasu matasa da ke aikata laifukan yanar gizo, suna amfani da kwamfuta wajen tuntuɓar jami’an gwamnati da mutanen da suke zaton suna da kuɗi domin damfararsu.

“An riga an kama wasu daga cikinsu. Su ne dai waɗanda suke kiran kansu “‘Yan Vocal”.

Waɗannan ‘Yan Vocal ne yanzu ake kira da suna Sai Malam.”Kwamishinan ya jaddada cewa hukumomin tsaro na ci gaba da sa ido domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Kebbi.

Kebbi
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi
  • Sulaiman
    An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya
  • Sulaiman
    Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin
  • Sulaiman
    Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

MASU ALAKA

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola
Manyan Labarai

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa
Manyan Labarai

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Next Post
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Jagorancin Siyasar Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Jagorancin Siyasar Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

Manchester Derby: City Ta Nunawa United Kwanji A Old Trafford

September 13, 2026
Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

September 13, 2026
Ka Kyale Ni Nayi Wa Mutanen Binuwai Aiki – Gwamna Alia Ga Ortom

Makiyaya Sun Yi Asarar Shanu 200,000 Ta Dalilin Rikice-Rikice – MACBAN

September 13, 2026
Kebbi

Farashin Man Fetur Ya Sake Tashi A Abuja

September 13, 2026
Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

Shugabannin BRICS Sun Amince Da Sanarwar Hadin Gwiwa A Taron Koli Na New Delhi

September 13, 2026
Kebbi

Malamai Da Limamai 3,000 Sun Yi Addu’ar Zaman Lafiya Da Nasarar Tinubu A 2027

September 13, 2026
An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

An Samu Babban Sakamako Kan Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa Na Duniya

September 13, 2026
Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

Ministan Kimiyya Na Afirka Ta Kudu Ya Yi Kiran Zurfafa Hadin Gwiwar Kimiyya Da Fasaha Da Sin

September 13, 2026
Kebbi

An Gudanar Da Sallar Zana’idar Tsohon Gwamnan Gongola

September 13, 2026
Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.