ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Birtaniya

Jakadan Birtaniya mai barin gado a Nijeriya, Richard Montgomery, ya bayyana a ranar Talata cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ya aiwatar za su sanya Nijeriya ta samu ingantacciyar makoma na tsawon lokaci.

Montgomery ya ce duk da cewa wadannan sauye-sauyen sun jawo wa talakawa wahalhalu na dan lokaci, suna da matukar muhimmanci wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Mai bai wa Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS) shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Dakta Zacch Adedeji, Dare Adekanmbi, ya bayyana cewa jakadan ya fadi hakan ne a Abuja yayin ziyarar ban kwana da ya kai Hedikwatar Hukumar Tara Haraji.

ADVERTISEMENT

Jakadan ya ce: “Kasancewa a Nijeriya tsawon shekaru uku a lokacin da abubuwa masu kyau da dama suka faru abin burgewa ne kwarai.”

Ya ci gaba da cewa: “Na san cewa sauye-sauyen tattalin arziki suna da wahala, kuma suna iya jawo wa talakawa kuncin rayuwa na dan lokaci, kamar rage darajar kudi, hauhawar farashi da makamantansu.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

“Amma ina ci gaba da bayyana wa gwamnatinmu, har da sabon Firayim Ministanmu, Andy Burnham, wanda ke fatan tattaunawa da Mai Girma Shugaba Bola Tinubu cikin makwanni masu zuwa, irin muhimmancin wadannan sauye-sauyen.

“Ko aikin da Yemi Cardoso ya yi a Babban Bankin Nijeriya (CBN), ko wanda Wale Edun ya fara a Ma’aikatar Kudi, da kuma aikin da kai (Zacch Adedeji) da Taiwo Oyedele, wanda yanzu shi ne Ministan Kudi kuma Ministan Daidaita Tattalin Arziki, kuka yi wajen gyaran tsarin haraji da tafiyar da harkokin kudaden gwamnati abin a yaba ne.

“Na san Nijeriya kasa ce mai sarkakiya. Na kuma san tsara kasafin kudi da tafiyar da kudaden gwamnati abu ne mai wahala saboda yadda tsarin kasafin kudi ke gudana a Majalisar Dokoki ta Kasa.

“Saboda haka, ina ganin abin da ministocin kudi da kai da tawagarka kuka yi wajen dora Nijeriya kan turba mai kyau da kuma inganta yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati abin yabawa ne kwarai.

“Na yaba ba wai kawai da kwarewar fasaha ba, har ma da hikimar siyasa da tawagarku ta nuna wajen gudanar da wadannan sauye-sauyen.

A cikin shekara ukun nan, abin farin ciki ne ganin an samar da sabuwar tawaga a NNPCL, an jawo karin masu zuba jari, kuma kimar amincewar masu ba da bashi ga Nijeriya ta inganta.

“Ina ganin abin da ku da sauran manyan jami’an da ke tafiyar da tattalin arzikin kasa kuka yi yana da matukar muhimmanci ga makomar Nijeriya. Don haka ina matukar yaba muku.

“Na sha fada wa wasu manyan jami’ai cewa shekaru hudu masu zuwa ya kamata su mayar da hankali wajen daga bunkasar tattalin arziki daga kashi 4 zuwa kashi 7 cikin dari, domin wannan ne zai kawo sauyi ga rayuwar talakawa. Kuma ina da tabbacin cewa tare da gudummawarku da ta sauran masu ruwa da tsaki, hakan zai yiwu.”

Montgomery ya bayyana Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS) a matsayin daya daga cikin mafi kyawun abokan huldar Birtaniya, tare da yabawa Adedeji kan yadda yake gudanar da aiki mai wahala amma mai amfani.

Haka kuma, ya yaba da hadin gwiwar da ke tsakanin NRS da Hukumar Tara Haraji ta Birtaniya (HMRC) wajen yin bitar tsarin aiki da musayar kwarewa.

A nasa jawabin, Shugaban NRS, Dakta Zacch Adedeji, ya ce abin takaici ne yadda Montgomery ke barin Nijeriya a wannan lokaci, tare da yabawa yadda ya gudanar da aikinsa.

Ya ce: “Yadda ka gudanar da wannan aiki ya sauya labari gaba daya, musamman irin goyon bayan da ka ba mu, na kai tsaye da kuma ta fuskar taimakon fasaha wajen aiwatar da sauye-sauyenmu.

“Wannan goyon baya ba zai taba gushewa daga zukatanmu ba. Ina kuma gode maka da jajircewarka da sadaukarwarka.

“Ko da yake kana barin Nijeriya, kana iya ganin wasu daga cikin kyawawan sakamakon wadannan sauye-sauyen.

“Ka dauke mu a matsayin wasu muhimmin bangarori na tsarin tattalin arzikin Nijeriya, kuma irin wadannan tattaunawa sun taimaka sosai wajen tsara sauye-sauyenmu.

“Na kuma yarda da abin da ka ce cewa ci gaba mai dorewa ba ya dogara da bayar da tallafi kawai, sai dai a kan kulla hadin gwiwa mai amfani. Ina da tabbacin cewa irin wannan kyakkyawar alaka za ta ci gaba da kasancewa tare da wanda zai gaje ka.”

Birtaniya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000  A Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000 A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.