ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bincike Ya Nuna Ƙungiyar Da Ta Zargi Gwamna Lawal Da Yi Wa ’Yan Bindiga Afuwa Ta Bogi Ce

by Sulaiman
9 months ago
Gwamna Lawal

An gano cewa zargin da ake yaɗawa cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi afuwa tare da sakin ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci ba shi da tushe kwata-kwata, bayan cikakken bincike da jaridar PremiumTimes ta gudanar kan batun da ya tayar da ƙura a kafafen yaɗa labarai.

A ranar 28 ga Nuwamban 2025, wata ƙungiya mai suna ‘Human Rights Watchdog in Africa’ (HRWA) ta fitar da wata sanarwa da aka ce daraktanta, Samson Adamu, ne ya sanya wa hannu, inda ta buƙaci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara, bisa zargin cewa Gwamna Lawal ya yi afuwa tare da sakin ’yan bindiga 69 ta sirri, ƙarƙashin wani shiri da ta kira ‘Religious Amnesty.’

ADVERTISEMENT
  • Rashin Tsaro: Tinubu Ya Bada Sabbin Umarni Ga Shugabannin Sojoji
  • Gwamna Yusuf Ya Ziyarci Ƙananan Hukumomi 2 Kan Harin ‘Yan Bindiga A Yankunan 

Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa ba a samu asalin wannan sanarwa daga kowace sahihiyar majiya ba. Ƙokarin samun kungiyar HRWA da shugabanta Samson Adamu ya ci tura, domin babu wani ofishinta, lambar waya, shafin yanar gizo ko kuma rajistarta da aka samu a Hukumar Kula da Kamfanoni da Ƙungiyoyi ta Ƙasa. Haka nan, babu wani sahihin bayani ko sahihiyar shaidar da ke nuna wanzuwar ƙungiyar ko wannan mutum kafin ƙarshen Nuwamban 2025.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Bincike ya kuma tabbatar da cewa abin da ya faru a zahiri shi ne Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara ta taimaka wajen biyan basussukan fursunonin da aka yanke wa hukunci a shari’o’in farar hula, wanda hakan ya taimaka wajen sakin mutum 909 daga 2024 zuwa 2025. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sakataren Zartarwa na hukumar, Habib Muhammad Balarabe, a wani taron ƙarshen shekara da aka gudanar a Gusau.

A cewarsa, a 2024 kaɗai, an biya basussukan fursunoni 473, yayin da a 2025 aka kashe Naira miliyan 67.2 domin biyan basussukan mutum 436, wanda adadin gaba ɗaya ya kai 909 cikin shekaru biyu. Hukumar ta kuma bayar da tallafin jari ga mata 200 ƙanana ‘yan kasuwa da Naira dubu 50-50, tare da bai wa wasu mata 100 kayan fara sana’a bayan kammala horarwar kiwon kaji na makonni uku.

Jami’an hukumar Zakka sun bayyana cewa, ayyukansu na jinkai ba su taba shafar ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci kan laifukan ta’addanci ba. Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, abin dariya ne ace gwamnan da ya sha bayyana a fili cewa ba ya sulhu da ‘yan bindiga shi ne zai koma ya sake su bayan an yanke musu hukunci.

Haka kuma, an tabbatar da cewa Gwamna Lawal bai taɓa sauya matsayarsa kan batun ‘yan bindiga ba. A ranar 29 ga Oktoban 2025, yayin da yake jawabi a gaban ɗaliban kwas ɗin tsaro a ‘National Institute for Security Studies’ da ke Abuja, gwamnan ya bayyana adawarsa ga yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga da ake yi a wasu jihohin Arewa maso Yamma, yana mai cewa sulhu ba tare da ƙwace makamai ba hanya ce ta jinkirta tashin hankali.

Kakakin gwamnan, Suleman Bala Idris, ya musanta zargin baki ɗaya, yana mai cewa labarin ƙirƙirarre ne da wasu ‘yan siyasa da ke cikin matsin lamba suka tsara domin ɓata sunan gwamnatin Zamfara.

Ya jaddada cewa, babu wani lokaci da Gwamna Lawal ya yi afuwa ko ya saki kowane ɗan bindiga daga kurkuku.

Bayan kammala bincike mai zurfi, an tabbatar da cewa ƙungiyar HRWA da shugaban nata kamar fatalwa ne, kuma zargin da aka yi cewa Gwamna Lawal ya saki ‘yan bindiga ƙarya ne tsagwaron gaske.

Gwamna Lawal
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Next Post
2027: Ba Mu Da Hujjar Juyawa Gwamna Uba Sani Da Tinubu Baya — Tsohon Gwamnan Kaduna

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.