Akasarin ‘yan Nijeriya tambayar da har yau suke neman amsarta shi ne, shin tulin basukan da kasar ke karbo, na taimaka wa, wajen bunkasa kasar ko dai, ana karbo basukan ne, domin ci gaba da dorewar rayuwa.
Ko da yake dai, Nijeriya na da burin ganin ta samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasarta, kamar yi masu Tituna, samar da wutar lantarki, gina makarantu, inganta kiwon lafiya da sauransu.
Gwamnatocin baya da suka shude na kasar, akasari sun dogara ne, waejn samun kudaden shiga na cikin gida, bangaren zuba jari na masu zaman kansu da wasu basuka daga waje, domin cimma burinta.
Sai dai, bukatar gwamnatin kasar na sake ciwo wani bashin dala biliyan 1.25 daga gun Bankin Duniya, ya haifar da ce-ce kuce.
Amma a nan za a iya cewa, kusan cewao bashi, Hanji ne ga kasashen masu karamin karfin tattalin arziki, wanda hatta suma wasu kasashen da ake kira sun ci, gaba, ba a bar su a baya, wajen ciwo bashi na dogon zango ba.
Babban abin tsoro ga ciwo bashi shi ne, zai iya kasancewa, za a bar wa ‘yan baya masu tasiwa, nauyin biyan basukan da mai yuwa, ba su da masaniyar ciwo bashin.
Sai dai, Bankn na Duniya za a iya cewa, ya yi azarbabi wajen kare Nijeriya na ciwo bashin, duba da ikirarinsa na cewa, bashin zai taimaka wa Nijeriya a bangaren zuba jari, samar da ayyukan yi, habaka fannonin aikin noma, samar da sauye-sauyen fasahar zamani da sauransu.
Wannan manufar da ake son cimma, a rubuce, zai yi matukar wuya, a iya sukar ta, haka tabbas, Nijeriya na cikin bukatar fadada tattalin arzikinta da samar da ayyukan yi, duba da yadda yawan ‘yan kasar, ke kara karuwa.
A gafe daya kuma, alummar kasar, na ci gaba da jefa shakku a zukakanta kan yadda bashin da ake ciwo, ke kara karuwa, musamman a shekaru da dama, da suka gabata, amma kuma a gefe daya, a zahiri ana ganin wasu manyan kayan kasar, na ci gaba da lalacewa da karuwar rashin aikin yi ga kuma fatara da talauci da suka yiwa talakawan kasar, kamari.
Bugu da kari, akasarin ‘yan kasar na ci gaba da nuna damuwarsu, game da gaskiyar da bin ka’ida, kan ciwo bashin, inda kuma suke bukatar sanin shi adadin bashin da za a karbo, kuma sauran basukan da aka ciwo a baya, shi me aka yi da su.
Inda ace, duk basukan da ake karbowa ‘yan kasar na gani a kas, musamman wajen samar da ayyukan yi, da za a iya cewa, karbo bashi, na da tasiri.
Sai dai, duba da cewa, kusana ana ciwo basukan ne, domin a ciki gibin da ake da shi, musamman na kasafin kudin kasar, to za iya cewa, tamkar mayar da hannun Agogo baya ne kurum.
Akasarin basukan da ake karbowa, ana barin gwamnati mai zuwa da kuma ‘yan kasar da ke biyan harji, da biya ne.
Hakan dai, na ci gaba da tuna asirin bangaren masu kirkiro da dokokin kasar ne.
A Nijeriya dai, an shafe shekaru, ana faro ayyuka, amma daga baya, a yi watsi da su.
Ya zama wajbi, ‘yan Nijeriya su nuna tirjiya kan duk wani bashi da za a karbo, matukar ba za a yi amfani da shi, yadda ya dace ba.
Haka zalika, ya zama dole gwamnati, ta tabbatar da tana yin gaskiya da bin ka’ida, wajen kashe kudaden kasar kan ayyukan da za su amfani ‘yan Nijeriya.
Ya kamata duk wani bashi, a rinka auna nayinsa, kafin a ciwo shi, kuma ‘yan kasa, suma sun rinka auna, da kuma sanya ido, kan me aka yi da bashin.
Mai yuwa, bashin na baya-bayan da gwamnatin ke son karbowa daga gun Bankin Duniya, zai iya taimaka wa, fannin samar da sauye-sauyen fannin tattalin arzikin kasa da zuba jari.
Koma dai menene alfanunsa, kowanne irin bashi, ya danganta ne, kan yadda aka wanzar da shi da kuma ka’idar da aka bi, wajen yin amfani da shi, domin samun sakamako na gari.
Tambayar da ita kanta Nijeriya ya wajaba ta yiwa kanta shi ne, ta na ciwo bashi ne, domin kawai amfanin yau.
Sai dai, bashin na baya-baya da kasar ke son karbowa daga gun Bankin Duniya, shi ne, zai fayyace Aya da Tsakuwa, kan yadda aka tafiyar da shi.Dabarai dai, inji masu iya Magana, ta rage ga mai shiga Rijiya.













