A cikin wannan shekarar, kasar Sin ta fuskanci matsanantan ibtila’o’i na yanayi a-kai-a-kai. Hukumomi a dukkan matakai sun tsara ayyukan rigakafi, da rage radadi, da ba da agajin ibtila’i cikin tsari mai inganci, domin rage asarar da ibtila’in ya haddasa da kuma tabbatar da kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a a mataki mafi girma da zai iya yiwuwa.
Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kafar CGTN ta gudanar a tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya ya nuna cewa, kashi 92.7 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun gamsu sosai da karfin kasar Sin wajen rigakafi, da rage radadi, da ba da agaji, kuma sun yi amannar cewa dabarar da kasar Sin ke amfani da ita tana koyar da darussa masu muhimmanci.
Aiwatar da ayyukan rigakafi, da rage radadi, da ba da agaji na kasar Sin bisa inganci ta samo asali ce daga kakkarfan goyon bayan tsarin hukumomi. A cikin wannan shekarar, kasar Sin ta fitar da shirin zamanantar da tsarin tunkarar abubuwa na gaggawa a kasar a lokacin aiwatar da shirin ci gaban kasa da inganta zamantakewa na shekaru biyar-biyar karo na 15 (2026-2030), wanda ya shimfida kyawawan tsare-tsare domin inganta tsarin kula da abubuwa na gaggawa, da karfafa cibiyoyin ceto, da habaka karfin sanya ido da yin gargadi da wuri kan abkuwar ibtila’i, gami da kyautata hukumomin ba da agajin gaggawa na kananan hukumomi.
A cikin binciken, kashi 94.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun yi amannar cewa wannan yana nuna kwarewar tsara al’amura da karfin aiwatarwa na kasar Sin a bangaren gina karfin rigakafi, da rage radadi, da kuma ba da agaji.
Bugu da kari, an samar da ingantaccen tsarin fasahar yin gargadi da wuri game da yanayi da kasar Sin ta kera mai suna “Mazu” a kasashe bakwai ciki har da kasar Pakistan, sannan sama da kasashe 40 ne a fadin duniya ke amfani da samfuran tsarin fasahar yin gargadin na “Mazu”.
A game da wannan, kashi 91.1 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyi sun yi amannar cewa wannan yana jaddada matsayin kasar Sin na sauke nauyin da ke wuyanta a matsayinta na babbar kasa, wajen taimaka wa kasashe masu tasowa domin su bunkasa karfinsu na rigakafi, da rage radadi, da kuma ba da agajin ibtila’i. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














