Jihar Katsina na tura wani gagarumin hadin kayan aikin tsaro, tattara bayanan sirri da matakan tsaro na al’umma, yayin da Gwamna Dikko Radda ke kokarin sake fasalin yadda jihar ke tunkarar matsalar ’yan bindiga.
A halin yanzu, jihar na da akalla motocin sulke 23 (APCs), wadanda suka fi yawan motocin sulke da kowace gwamnatin jiha ta mallaka, tare da motocin daukar kaya 200, daruruwan babura, jirage marasa matuki da dama, kayan sa ido da leken asiri, makamai da harsasai, da kuma cibiyar sa ido ta zamani.
Yawancin wadannan kayan aikin tsaro gwamnatin jihar ta mika su ga hukumomin tsaro na yau da kullum da ke aiki a Katsina, ciki har da rundunar sojoji da ’yansanda, da kuma sabuwar Rundunar Tsaron Al’umma (Community Watch Corps) da gwamnatin jihar ta kafa, wadda ke da mambobi 10,000.
Kara yawan kayan aikin tsaro wani bangare ne na abin da jami’an gwamnatin jihar suka bayyana a matsayin dabarar fannoni da dama wajen yaki da rashin tsaro, wadda ta hada da kayan aiki, jami’an tsaro, tattara bayanan sirri da kuma hada kan al’umma wajen harkokin tsaro.
Wakilanmu sun gano cewa Gidan Gwamnati na Katsina ne ke kula da sayen mafi yawan wadannan kayan aikin tsaron.
A cewar jami’an gwamnatin jihar, kara samun kyakkyawan hadin gwiwa da Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF) wajen sa ido, gano wuraren da ’yan bindiga suke boye da kuma fatattakar su daga dazuzzuka da wuraren duwatsu a wasu kananan hukumomin jihar, ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da aka samu kawo yanzu.
A watan Agustan 2025, Rundunar Sojin Sama ta kai samame kan wani sansanin ’yan bindiga da ke Dutsen Pauwa, a Karamar Hukumar Kankara, inda ta yi nasarar ceto mutane 76.
A karkashin Operation Fansan Yamma, Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta kuma lalata wani sansanin ’yan bindiga a Danfako, Karamar Hukumar Faskari, a watan Nuwamba 2025. Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na Rundunar, Ehimen Ejodame, ya ce an gudanar da aikin ne bisa bayanan sirri da aka tattara ta hanyar sa ido.
Haka kuma, Rundunar Sojin Sama ta lalata wata cibiyar ajiyar kayayyakin tallafi na ’yan bindiga da ke Dajin Dan-Aji a watan Mayun 2026.Wakilanmu sun kuma ga ayyukan sa ido da suka hada da tura jami’an Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya a manyan hanyoyin jihar. An dora wa jami’an alhakin sa ido kan zirga-zirgar baki daga kasashen waje, tare da yin musayar bayanai da juna a ainihin lokacin.
Katsina na daga cikin jihohin Nijeriya da dama da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar, abin da ya sa sa ido a kan manyan hanyoyin jihar ya zama muhimmin bangare na dabarun tsaron jihar.
Mataki na biyu na wannan dabarar ya kunshi sanya hannun jari wajen samar da jami’an tsaro, horar da su da kuma tattara bayanan sirri a cikin al’ummomi, da nufin hana ayyukan ’yan bindiga ta hanyar katse hanyoyin samun kayan tallafi ga masu aikata laifuka da kuma samar da hanyoyin daukar matakin gaggawa idan aka kai hari.
Muhimmin bangare na wannan tsarin shi ne rarraba dukkan kananan hukumomin jihar 34 zuwa rukuni uku bisa la’akari da matakin rashin tsaron da al’ummominsu ke fuskanta.
Dr. Nasir Mu’azu Dan Musa, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Gida, ya bayyana dalilin da ya sa aka rarraba kananan hukumomin zuwa yankuna masu fuskantar barazana da kuma yankunan da ba sa fuskantar rikici.
Ya ce wannan rarrabawar ita ce ke kayyade yawan albarkatu, jami’an tsaro da kayan aikin da za a tura, da kuma irin huldar tsaro da za a yi da al’ummomi a kowace karamar hukuma daga cikin 34.
Akalla kananan hukumomi takwas an ware su a matsayin yankunan, inda ’yan bindiga suka fi yawan ayyuka. Galibin wadannan yankuna na da dazuzzuka ko duwatsu, wadanda ke ba ’yan bindiga damar boyewa tare da sanya ayyukan jami’an tsaro su kasance masu wahala.
Wadannan kananan hukumomi sun hada da Jibia, Batsari, Safana, Dan Musa, Faskari, Sabuwa, Kankara da Sandamu. Wasu kananan hukumomi 11 kuma an ware su a matsayin yankunan da ke fuskantar barazana, yayin da sauran 15 aka dauke su a matsayin yankunan da ba sa fuskantar rikici.
Dr. Dan Musa ya ce gwamnatin jihar ta fahimci cewa matsalar ’yan bindiga tana da alaka da al’umma, don haka ta sanya al’ummomi a sahun gaba na dabarun tsaro, kafin tura rundunonin tsaro na yau da kullum.
Mataki na uku, wanda ke da alaka ta kut-da-kut da na biyu, shi ne kokarin Gwamna Radda na shigar da sarakunan gargajiya, kwararru a harkokin tsaro, malaman jami’o’i, malamai da shugabannin al’umma cikin tsarin tsara manufofi da ba da shawarwari.
Manufar hakan ita ce karfafa hadin gwiwa da kuma tabbatar da cewa ayyukan tsaro suna amfani da ilimin da ya samo asali daga cikin al’umma, tare da aiwatar da su a kowane mataki. Wadannan tsare-tsare sun hada da Kwamitin Ba da Shawara kan Tsaro da kuma wani Kwamitin Zaman Lafiya daban a kowace karamar hukuma.
A takaice, hadawa da tura kayan aikin tsaro, ayyukan da suka dogara da bayanan sirri, sa ido daga cikin al’umma, da kuma shigar da hukumomin gargajiya da na al’umma cikin harkokin tsaro, na nuna wani gagarumin sauyi a yadda Katsina ke tunkarar matsalar rashin tsaro.
Wannan sabon salo ne na neman hada karfin makamai na rundunonin tsaro na yau da kullum da kuma bayanan sirri da kusancin al’umma da wadannan jami’an ke da alhakin karewa.














