Abin da ci gaban Sin ya kawo ba barazana ba ce, sai dai riba mai amfani. Sakamakon wani binciken da kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ta fitar a tsakanin masu amfani da yanar gizo a fadin duniya ya nuna cewa, kashi 87% na masu bayyana ra’ayoyi sun yi imanin cewa, a cikin duniyar dake cike da rashin tabbas, Sin tana kara tabbaci ga harkokin cinikayya na duniya a matsayinta na “babbar mai sayar da kayayyaki” kuma “babbar mai sayen kayayyaki”.
Bugu da kari, kashi 89.8% na masu bayyana ra’ayoyin suna ganin cewa, Sin ta kirkiro guraben ayyukan yi da kudin shiga masu yawa, yayin da kashi 90.9% na masu bayyana ra’ayoyin suke ganin cewa Sin ta taimaka wa kasashen dake dogaro da albarkatu da fitar da kayayyaki wajen raya tattalin arzikinsu, wanda hakan ya inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya mai hada kai da kawo alheri ga kowa da kowa.
An fitar da wannan binciken ne a dandamalin CGTN guda biyar na harsunan Ingilishi da Sifaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda masu amfani da yanar gizo 8,864 suka jefa kuri’a tare da bayyana ra’ayoyinsu.(Safiyah Ma)














