Gwamnatin Birtaniya ta gargaɗi ƴan ƙasarta da su guji tafiye-tafiye zuwa Saudiyya waɗanda ba su da muhimmanci, sakamakon hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen ke kai wa ƙasar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ta shawarci ƴan ƙasar da su guji duk wata tafiya zuwa Saudiyya da ba ta zama dole ba, bisa la’akari da yanayin tsaro.Tun da farko, wasu ƙasashe da dama sun fitar da irin wannan gargaɗi ga ƴan ƙasashensu kan tafiye-tafiye zuwa Saudiyya.
Haka kuma, Ofishin Jakadancin Amurka da ke Saudiyya ya shawarci ƴan ƙasar Amurka da su yi taka-tsantsan yayin tafiye-tafiye, sakamakon hare-haren da aka kai kan filayen jiragen saman Saudiyya.
A cikin sanarwar tsaro, ofishin ya bayyana cewa amfani da motoci masu zaman kansu, jiragen ƙasa ko motocin bas na iya zama wasu hanyoyin da za a yi la’akari da su maimakon zirga-zirgar jiragen sama zuwa ko daga Saudiyya.














