Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce biyan wasu tsoffin basussukan da suka dabaibaye ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya ya fara dawo da amincewar masu ruwa da tsaki, tare da ƙarfafa tubalin samar da ingantaccen tsarin wutar lantarki a ƙasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin taya Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Nigeria Bulk Electricity Trading Plc (NBET), Akin Odeyemi, murnar zagayowar ranar haihuwarsa a ranar 31 ga Oktoba, 2026. Shugaban ƙasar ya yaba da rawar da Odeyemi ya taka wajen aiwatar da Shirin Shugaban Ƙasa na Rage Bashin Bangaren Wutar Lantarki.
Ya ce nasarar fitarwa da rattaba hannu kan takardun lamunin kuɗi na Naira biliyan 728.979, ƙarƙashin shirin samar da kuɗi na Naira tiriliyan huɗu, ta ba NBET damar biyan wasu kamfanonin samar da wutar lantarki da kamfanonin da ke samar musu da iskar gas. Ya bayyana cewa waɗannan basussuka da aka daɗe ana takaddama a kansu sun kasance cikin manyan matsalolin da suka rage amincewar masu samar da wuta da sauran masu ruwa da tsaki a harkar.
Tinubu ya ce an samu nasarar biyan bashin ne ta hanyar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da bin ƙa’idojin kula da kuɗi da haɗin gwiwa. Ya ƙara da cewa matakan sun taimaka wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin masu ruwa da tsaki da kuma samar da ginshiƙin ingantaccen kasuwar wutar lantarki.
Shugaban ƙasar ya bayyana Odeyemi a matsayin ƙwararren masani mai gogewa a fannin makamashi, da wutar lantarki, da bunƙasa ababen more rayuwa da harkokin kuɗi. Ya ce gogewarsa ta taimaka wajen jagorantar NBET, tare da yi masa fatan samun lafiya da ƙarin nasarori a hidimar ƙasa.














