ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, November 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

by CGTN Hausa
2 days ago
Xi

Da safiyar yau ranar 2 ga watan Nuwamba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Sultan na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said, wanda yake ziyarar aiki a kasar, a babban dakin taro na jama’a da ke birnin Beijing.

A ganawar tasu, Xi ya nuna cewa, Sin da Oman suna da daddaden zumunci dake da ingantaccen tushe da ma kyakkyawar makoma. Kuma Sin tana fatan hada hannu da bangaren Oman wajen ingiza dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu zuwa sabon mataki, ta yadda al’ummar kasashen biyu za su amfana da ita yadda ya kamata, kana da ba da gudummawa ta a zo a gani ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadatar yankunan.

Ban da wannan kuma, Xi ya jaddada cewa, ziyarar a wannan karo ta kasance ta farko da Sultan na kasar Oman ya yi a Sin cikin shekaru 48 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, ziyarar da za ta taka rawar gani a tarihin dangantakar kasashen biyu, da ma ingiza bunkasuwar dangantakar.

ADVERTISEMENT

Kazalika Xi ya nuna cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan na bukatar hadin gwiwar mabambantan bangarori. Ya ce Sin na fatan kara hadin gwiwa da kasashen Larabawa da mambobin kwamitin hadin gwiwar kasashen Gulf na GCC, da suka hada da Oman, domin yin kokari tare wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tun da wuri, da kuma samun zaman lafiya mai dorewa.

A nasa bangare kuwa, Haitham ya ce, Sin ta zama babbar kasa ta siyasa da tattalin arziki a duniya karkashin jagorancin shugaba Xi, kuma Sin tana ba da gudummawa mai muhimmanci ga wadata da kwanciyar hankalin duniya.

LABARAI MASU NASABA

Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

Ya ce, Sin da Oman na da daddaden zumunci, kuma suna ta girmama juna da amincewa da juna. A cewarsa, Oman tana bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma tana goyon bayan Sin wajen kare ikon mallakar kasa da cikakken yankinta.

Yana fatan amfani da zarafin wannan ziyara wajen habaka damammakin hadin gwiwa, da gina dangantakar abokantaka mai kyakkyawar makoma, da kuma ingiza samun ci gaban dangantakar kasashen biyu mai armashi.

Dadin dadawa, an ba da labarin cewa, a yayin ziyarar, bangarorin biyu sun fitar da “sanarwar hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyyar Jama’ar Sin da kasar Oman kan zurfafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu”.(Amina Xu)

Xi
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    An Bude Dandalin Baje Kolin Aladu Na Dunhuang A Yankin Arewa Maso Yammacin Sin

MASU ALAKA

Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet
Daga Birnin Sin

Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

November 3, 2026
An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

November 3, 2026
Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin

November 3, 2026
Next Post
Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara

Kano: An Kama ’Yan Kasuwa Bisa Zargin Ƙoƙarin Sauya Ranar Ƙarewar Amfanin Wata Madara

LABARAI MASU NASABA

ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

ADC Ta Ɓoye Wajen Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Atiku A Sakkwato Saboda Matsalar Tsaro

November 4, 2026
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Bashin Da Ake Ci Na Barazana Ga Tattalin Arziƙin Nijeriya – Sanusi II

November 4, 2026
Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa

Badakalar Rajistar Masu Zaɓe: Ezekwesili Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Mai Zaman Kansa

November 4, 2026
Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

Neman Bayani Game Da Jigon Kalmar ‘China+’ Na Kara Maimaituwa A Shafukan Intanet

November 3, 2026
Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya

Hanyar Abuja-Kaduna: Ci Gaban Aikin Gyara Ya Farfaɗo Da Fatan Matafiya

November 3, 2026
An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

An Gudanar Da Tattaunawar Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin Sin Da Ci Gaban Duniya A Washington D.C.

November 3, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Za Mu Biya Ma’aikata Alawus ɗin Sufuri na Naira 70,000 — Gwamnatin Kebbi

November 3, 2026
Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa

Tsadar Rayuwa: Yadda Iyalan Nijeriya Ke Komawa Abinci Mai Rahusa Domin Samun Sauƙin Rayuwa

November 3, 2026
Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin

Shugabannin Kasashen Waje Za Su Halarci Baje Kolin Hajojin Da Ake Shigowa Da Su Kasar Sin

November 3, 2026
Yadda Na Sayar Da Kadarori Na Don Ɗaukar Nauyin Ɗalibai A Ƙasashen Waje – Kwankwaso

APC Ta Musanta Zargin Kwankwaso Kan Cire Sunan Gwarzo A Jerin ‘Yan Takarar Gwamna A Kano

November 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.