ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 2, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago
Tinubu

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ƙalubalanci Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da su fafata a gasar karanta Alƙur’ani da kawo nassosin ayoyinsa, bayan ziyarar ibadar Umrah da shugaban ƙasar ya kai Saudiyya.

Melaye ya bayyana ƙalubalen ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026. Ya ce yana shirye ya fafata da Tinubu kan kawo nassosin Alƙur’ani da zarar shugaban ƙasar ya dawo daga Saudiyya.

A cikin saƙonsa, Melaye ya rubuta cewa: “Yanzu da Alhaji Bola Tinubu yake Umrah, da zarar ya dawo, ina ƙalubalantarsa da gasar kawo nassosin Alƙur’ani. Ba wanda zai yi wa Allah ba’a.” Wannan kalubale ya biyo bayan bayanan da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, ya wallafa game da ibadar da Tinubu ya gudanar a Saudiyya.

ADVERTISEMENT

A yayin ziyarar, Tinubu ya samu damar shiga cikin ɗakin Ka’aba da ke Makka domin yin addu’a. Shugaban ƙasar ya bayyana cewa ya roƙi Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa ’yan Nijeriya hidima, tare da addu’ar samun haɗin kai da wadata ga ƙasar.

Sai dai rahoton bai bayyana cewa Tinubu ya mayar da martani kan ƙalubalen Melaye ba. Haka kuma, Melaye bai yi cikakken bayani kan ƙa’idojin gasar ko lokacin da za a gudanar da ita ba.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

Tinubu
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
  • Abubakar Sulaiman
    Ba Za Mu Yarda Da Maguɗin Zaɓe Ba – Dino Melaye Ya Gargaɗi INEC
  • Abubakar Sulaiman
    Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa A 2027 – Barau
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Fara Farautar Maharan Da Suka Kashe Abokin Aikinsu A Filato

MASU ALAKA

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi
Labarai

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

November 2, 2026
Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni
Da ɗumi-ɗuminsa

Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

November 2, 2026
INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI
Manyan Labarai

Zaɓen 2027: Shin INEC Za Ta Iya Dawo Da Aminci A Zukatan Jama’a Kan Bayyanar Rajistar Zaɓe Ta AI?

November 2, 2026
Next Post
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

Xi Jinping Ya Tattauna Da Sultan Na Oman Haitham Bin Tariq Al- Said

November 2, 2026
Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

Sojoji Sun Kuɓutar Da Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Kebbi

November 2, 2026
Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani

Dino Melaye Ya Ƙalubalanci Tinubu Gasar Karanta Alƙur’ani

November 2, 2026
Shin Wannan Ce Shekarar Da “Kano Pillars” Za Su Sake Lashe Kofin NPFL?

Shin Wannan Ce Shekarar Da “Kano Pillars” Za Su Sake Lashe Kofin NPFL?

November 2, 2026
Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

Yusuf Ya Miƙa Sunan Sunusi Bature Da Tsohon Kakakin Majalisa Gani Domin Naɗa Su Kwamishinoni

November 2, 2026
INEC Ta Fara Gyaran Rajistar Masu Zaɓe Bayan Zargin Amfani Da Hotunan AI

Zaɓen 2027: Shin INEC Za Ta Iya Dawo Da Aminci A Zukatan Jama’a Kan Bayyanar Rajistar Zaɓe Ta AI?

November 2, 2026
Ba Za Mu Yarda Da Maguɗin Zaɓe Ba – Dino Melaye Ya Gargaɗi INEC

Ba Za Mu Yarda Da Maguɗin Zaɓe Ba – Dino Melaye Ya Gargaɗi INEC

November 2, 2026
Yawaitar Tashin Gobara A Kasuwannin Kano, Shin ’Yan Kasuwa Na Samun Kulawar Da Ta Dace?

Yawaitar Tashin Gobara A Kasuwannin Kano, Shin ’Yan Kasuwa Na Samun Kulawar Da Ta Dace?

November 2, 2026
Tinubu Ne Zai  Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa A 2027 – Barau

Tinubu Ne Zai Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa A 2027 – Barau

November 2, 2026
Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaki Ya Rasu A Hatsarin Mota Watanni Uku Bayan Zaɓansa

Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaki Ya Rasu A Hatsarin Mota Watanni Uku Bayan Zaɓansa

November 2, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.