Cibiyar yaki da annobar cututtuka da kandagarkinsu ta Afirka (Africa CDC) ta yaba wa kasar Sin bisa goyon bayan da ta bayar ga kasashen Afirka dangane da shawo kan barkewar cutar Ebola mai lakabin Bundibugyo.
Babban daraktan cibiyar ta CDC Jean Kaseya ne ya bayyana hakan, bayan wata ganawa da Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a kungiyar tarayyar Afrika (AU), a hedkwatar hukumar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
A yayin taron, jami’an biyu sun rattaba hannu kan takardar mika tallafin gaggawa na karin dala miliyan 2.5 daga gwamnatin kasar Sin domin yaki da cutar Ebola a Afirka, lamarin da ya sa jimillar tallafin kai-tsaye da kasar Sin ta bayar ya karu zuwa dala miliyan 4.5, kamar yadda Kaseya ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X.
Bugu da kari, tawagar kwararrun likitocin kasar Sin rukuni na biyu da ke yaki da annobar cuta ta isa Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC), a farkon wannan watan nan domin karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen rigakafi da kuma shawo kan cutar ta Ebola. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)














