ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tasirin AI (Artificial Intelligence) A Harkokin Al’umma Na Yau Da Kullum

by Muhammad Bakir Bello
2 months ago
AI

A wannan makon mun nemi jin ta bakin masu karatunmu ne, kan yadda fasahar zamani ta AI (Artificial Interilligence) ke taka rawa a rayuwarsu. Ga dai ra’ayoyin kamar yadda Muhammad Bakir da Sani Anwar suka kawo mana.

Amina Bello daga Jihar Kaduna

AI (Artificial Intelligence), na da tasiri sosai a harkokina na yau da kullum da suka hada da:

ADVERTISEMENT

1- Kasuwanci: AI na taimaka min wajen rubuta tallace-tallace, tsara tambarin kasuwanci da kuma amsa tambayoyin kwastomomi cikin sauri.

2- Ilimi: Yana taimaka min, wajen yin bincike, fahimtar darussa, da kuma koyon sabbin abubuwa.

LABARAI MASU NASABA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

3- Sadarwa: AI na iya fassara min harsuna, gyara rubutu da kuma taimakawa, wajen rubuta sakwanni ta imel. Kamar a kasuwancina na sayar da turare da kayan kamshi, AI na taimaka min wajen: Rubuta kyawawan tallace-tallace.

Kirkirar tambari da hotunan talla.

Ba da ra’ayoyin yadda za ka kara yawan kwastomomi.

Shirya sakwannin WhatsApp, Facebook da Instagram, domin tallata kayanka.

Muktar Anwar

Babu shakka, AI kan taimaka min ta fuskoki mabanbanta da suka hada da batun bincike na ilimi, mu’amaloli da suka shafi harkar samun ‘yan sulalla da sauran makamantansu.

Sai dai, dogara da AI kadai kacokan ba tare da tuntubar wasu majiyoyi tabbatattu ba, na da ‘yar matsala musamman a kan abin da ya shafi bincike na ilimi kai-tsaye, kasantuwar wasu lokutan a kan samu wasu iyan kura-kurai tattare da ita.

Yusuf Muhammad, daga Jihar Kano

Kirkirarriyar basirar Dan’adam ta zamani (Artificial Intelligence), ta yi matukar tasiri a rayuwata da kuma rayuwar mutane da dama.

Wata hanya ce ta koyar da bincike cikin manyan kayan aikin bincike da koyo mafi ci gaba da aka taba samu. Tana taimaka min, wajen yin tunani mai zurfi, koyon abubuwa cikin sauri da kuma gina sabbin fasahohi cikin sauki da inganci.

Buhari Abdullahi daga Jaji Jihar Kaduna

Ina amfani da AI musamman a bangaren kasuwanci na zamani (cryptocurrency), AI yana taimaka min wajen yin nazarin kasuwa ta hanyar binciken farashin kudaden dijital, gano yanayin canjin kasuwa da kuma taimaka min, wajen yanke shawara bisa matakan da zan dauka.

Haka kuma, akwai wasu manhajoji da ke amfani da AI wajen sa ido kan kasuwa, gano yiwuwar hadari da kuma gudanar da ciniki ta otumatik, bisa ka’idojin da mai amfani ya tsara.

Duk da haka, AI ba shi da ikon tabbatar da riba ko hasashen kasuwa daidai-wadaida a kowane lokaci, saboda kasuwar (cryptocurrency), na da matukar sauyin farashi da hadari.

Hamid Awwal, daga Jihar Kwara

Amatsayina na dalibi, AI yana taimaka min wajen karatu da yin bincike cikin sauki da kuma karancin lokaci, musamman wajen yin ‘project’, AI yana taimaka min sosai wajen samun littattafai, wadanda suka danganci fannin da nake bukata, hatta a karatuna yanzu na fi fahimtar karatu idan na yi amfani da AI, saboda yana yin bayani da kyau yana kuma kawo misalai sosai, sannan kuma yana amsa duk tambayin da za ka yi masa ba tare da bata lokaci ba.

 Ibrahim Aminu daga Zaria Jihar Kaduna

AI (Artificial intelligence), na da tasiri mai girma a ayyukan kasuwancina na yau da kullum, domin yana taimaka min wajen yin aiki cikin sauri da inganci.

Mussaman a fannin kafafen yada labarai, daukar hoto da tallan kasuwancina, ina amfani da ita wajen kirkirar taken rubutu da rubuta rahotanni da kirkirar dabarun tallan kasuwanci da gyara hotuna da bidiyo da kuma taimaka min wajen kai wa ga abokan ciniki da dama ta yanar yanar gizo.

Haka kuma, AI na taimaka min ta hanyar ba da amsa da sauri ga tambayoyi da kuma taimaka wa kasuwanci su fahimci abin da abokan ciniki ke so.

A cikin kasuwancina na buge-bugen takardu, AI na taimakawa wajen tsara ‘flyers, banners’, katin kasuwanci, takardun shaida, da sauran kayan tallace-tallace cikin sauki. Zai iya ba da shawarar tsarin zane, gyara kuskuren rubutu, inganta ingancin hoto da kuma sarrafa ayyuka ba ta re da bata lokaci ba.

Ta hanyar amfani da kayan aikin AI, zan iya kara yawan aiki, inganta ingancin aikina, jawo hankalin abokan cinikai da yawa da kuma yanke shawarar kasuwanci mafi kyau, bisa bayanai da yanayin kasuwa da take bayarwa.

Omar Abbas Sa’ad, daga Jihar Nasarawa

Yadda AI ke taimaka min wajen saukaka ayyukana na yau da kullum sun hada da kamar haka:

Sana’o’i uku nake yi a lokaci daya: Dan jarida, Telan zamani, kuma ina harkar gidaje. Abin da ya hada wadannan sana’o’i duka wuri guda a yau shi ne, amfani da fasahar AI.

A matsayina na dan jarida, AI ya zama abokin bincikena da kuma rubutuna. Idan na yi tunanin abin da nake so na yi, AI yana taimaka min wajen fadada shi tare da samun cikakken bayanai, kan abin da nake son aiwatarwa. Shi ya sa, abin da zai dauke ni tsawon awanni, idan na yi amfani da AI cikin ‘yan mintuna na kammala shi.

Kazalika, a matsayina na Telan zamani, AI yana matukar taimaka min, wajen fitar sabbin kaloli tare da zane iri daban-daban na dinkunan zamani. Sannan, AI yana taimaka min wajen kirkirar zane-zane, wadanda ma ban taba zaton zan iya samun su ba.

Haka zalika, yana taimaka min wajen binciko zane-zanen da sauri tare da gwada ra’ayoyi abokanan cinikina da kuma daidaita gaba da baya kafin a dinka.

Sannan, a matsayina na mai harkar cinikin gidaje, AI yana taimaka min, wajen yin tunanin yadda zan tallata hajata. Duk wata matsala da na nemi taimakonsa a kai, kama daga kan gidaje, wuri ko abokin ciniki, ba tare da wani bata lokaci ba, yana ba ni mafita mafi kyau.

Haka nan, batun isar da sako ga abokan ciniki tare da jawo hankalinsu. Yana kuma taimaka min wajen shirya ayyuka ta hanyar da za ta yi magana kai tsaye da masu saye da kuma masu zuba jari.

AI
Muhammad Bakir Bello
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?
Taskira

Mene Ne Ra’ayinku Kan Shigar Mata Harkokin Siyasa Gadan-gadan?

September 5, 2026
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?
Taskira

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

August 29, 2026
Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?
Taskira

Tsakanin Digiri Da Sana’a Wanne Ya Fi Muhimmanci A Wannan Lokacin?

July 25, 2026
Next Post
Sin Ta Nuna Matukar Adawa Da Matakin Burtaniya Na Mallake Kamfanin Karafa Na British Steel

Sin Ta Nuna Matukar Adawa Da Matakin Burtaniya Na Mallake Kamfanin Karafa Na British Steel

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.