Domin aiwatar da manufofin muhimmin jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping da ya gabatar a wurin bikin bude “Taron Fasahar AI na Duniya na shekarar 2026” da kuma “Taron Manyan Jami’ai kan Kula da Tafiyar da Sha’anin AI a Duniya,” an kaddamar da “Bikin Taron Fasahar AI na Sin na shekarar 2026”, wanda rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Sin, watau CMG da wasu hukumomi daban-daban suka shirya cikin hadin gwiwa a birnin Shanghai, yau Asabar 18 ga watan Yuli.
Shen Haixiong, shugaban CMG, ya halarci taron. A cikin jawabinsa, ya bayyana cewa CMG zai yi amfani da wannan dama mai tarihi wajen karfafa hadewar ci gaban fasaha da bunkasar al’adu cikin kwanciyar hankali, tare da yin hadin gwiwar samar da makoma mai haske inda fasahar kere-keren zamani za ta zamo mai amfanarwa da kuma kyautata rayuwar bil’adama a doron kasa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)













