ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Burina Zama Daya Daga Cikin Fitattun Masu Daukar Hoto A Nijeriya –Ibrahim Aminu

by Muhammad Bakir Bello
2 months ago
Hoto

A daidai lokacin da wasu matasa ke jiran sai sun samu aikin gwamnati bayan kammala karatu shi Ibrahim Aminu ya gwammaci ya fuskanci samar wa kanshi aikin yi ne domin dogaro da kansa. A tattaunawarsa da Wakilinmu Muhammadu Bakir Bello, ya bayyana yadda yara fada sana’ar daukar hoto na zamani. Ya kuma bayyana irinin nasarororin da ya samu da kuma irin burin da yake da su a nan gaba. Ga dai yadda hirar ta kasance:

Za mu so mu san takaitaccen tarihinka?

Sunana Ibrahim Aminu, an haifeni a garin Samaru, Zaria, Jihar Kaduna, Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Na fara karatuna a Foundation Nursery and Primary School, sannan sai na shiga Demonstration Secondary School wanda take Jami’an Ahmadu Bello Zaria, inda na kammala karatun sakandare. Na yi diploma a ‘Library and Information Science’, ‘Diploma in Adult Education’, da kuma bangaren aikin jarida ‘Diploma a Mass Communication’,

Bayan samun wadannan diflomomi uku, ban tsaya ba. Na ci gaba da karatu zuwa matakin digiri a Nuhu Bamalli Polytechnic Zaria, a fannin ‘Mass Communication’. A can ne na kara fahimtar muhimmancin sadarwa, daukar hoto, gyaran bidiyo da kuma yadda kafafen yada labarai ke tasiri a rayuwar mutane. Na kuma yi bautar kasa NYSC a Jihar Kano.

LABARAI MASU NASABA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

Ta yaya ka tsinci kanka a wannan sana’ar daukar hoto?

Na fara sha’awar daukar hoto ne tun ina kallon yadda ake daukar hotuna da bidiyo a wurare daban-daban kamar wajen bukukuwa da tarurruka. Daga baya na fara bincike a kan internet da YouTube don koyon dabarun daukar hoto. Na fara amfani da wayar hannu, sannan na kuma na fara aron kyamara daga abokan aiki. Na kuma samu dama ta aiki tare da wasu kwararrun masu daukar  hoto a Zaria. Na bi su zuwa taruka, tun ina daukar kayan aiki, har zuwa lokacin da suka koyar dani yadda suke gyara hotuna. A hankali a hankali na fara samun kwarewa har na iya tsayawa da kaina wajen daukar hoto da bidiyo.

Zuwa yanzu ka yi shekara nawa kana wannan sana’a?

Na shafe shekaru akalla kimanin shekara biyar zuwa shida ina gudanar da wannan sana’a. A cikin wadannan shekarun, kowace shekara ina koyan sabbin abubuwa.  A wata shekara na koyi yadda ake gyaran hoto da Photoshop, wata kuma na koyi yadda ake daukar bidiyo mai inganci da kuma yin editing da manhajar Premiere Pro.

Ba abu ne mai sauki ba, saboda fasaha tana canzawa kullum. Amma ina mai imani cewa dole mutum ya ci gaba da koyo idan kana son kasancewa a gaba. Shi ya sa har yau ina zuwa horo da kuma kallon sabbin dabaru na yadda ake aikin.

Ta yaya ka iya hada karatu da zirga-zirgar sana’ar daukar  hoto?

Wannan tambaya ce da mutane da yawa ke yi mini. Gaskiya sirrin shi shi ne tsara lokaci da jajircewa. Ina da jadawali na. Idan ina makaranta, ina ba da cikakken hankali ga karatu. Ban hada karatu da wani abu ba saboda ina son in fito da sakamako mai kyau.

Amma a lokutan da ba na da darasi, Kamar karshen mako, da kuma lokacin hutu, nakan gudanar da ayyukan daukar hoto. Wani lokaci ina yin aiki a safe sannan in koma karatu da yamma.

Tsari, addu’a da kuma goyon bayan iyaye ne suka taimaka min sosai. Alhamdulillahi na samu nasara a bangarorin biyu.

Mene ne bambancin tsarin daukar hoto na ANALOG da DIGITAL?

Wannan bambanci ne mai girma. Tsarin Analog shi ne tsohon tsari. Yana amfani da fim na musamman wato film. Bayan ka dauki hoto sai ka kai fim din a dakin gyara domin a wanke shi kafin ka ga sakamakon. Matsalar shi ita ce idan ka yi kuskure ba za ka iya gyara ba, sai ka sake dauka. Kuma yana cin lokaci da kudi.

Amma tsarin Digital kuwa na zamani ne. Yana amfani da kyamarorin dijital da wayoyin hannu masu inganci. Amfanin shi ne ka dauka ka gani nan take. Idan ba ka so, ka share ka sake dauka. Haka kuma zaka iya gyara shi cikin sauki da kwamfuta ko waya ta amfani da apps da software.

A wannan zamanin, tsarin Digital ya fi karfi kuma ya fi amfani saboda sauri, rahusa, da kuma inganci. Kusan duk masu daukar hoto a yanzu sun koma Digital.

Wasu irin kalubale ka fuskanta?

To kalubalen dana fuskanta suna da yawa musamman a farko. Na farko shi ne rashin kayan aiki masu inganci. Kyamara mai kyau a yanzu tana iya kaiwa rabin miliyan ko ma fiye da haka. Haka kuma lighting, tripod, da sauran kayan suna da tsada.

Na biyu kuma shi ne kudin gudanarwa. Wani lokaci kana da aiki amma babu kudin da za ka je wurin ko ka biya ma mataimaka.

Na uku kuma shi ne gasa da wayoyin hannu. Yanzu kowa yana da waya mai kyau mai daukar hoto. Don haka wasu mutane suna ganin ba su bukatar mai daukar hoto na musamman.

Amma da hakuri, addu’a da dagewa na samu damar shawo kan wadannan. Na fara da kadan, na ajiye kudi, na sayi kayana kadan-kadan har na kai inda nake yanzu.

Wasu irin nasarori ka samu a wannan sana’a?

Alhamdulillahi nasarori sun yi yawa. Na samu damar daukar hotuna da bidiyo a manyan taruka da bukukuwa a ciki da wajen Zaria. Na samu damar yin aiki da manyan mutane da kamfanoni.

Sana’ar ta bude min kofa ta sanin mutane masu muhimmanci. Na yi tafiye-tafiye zuwa garuruwa da dama saboda aiki. Wannan ya kara min kwarewa da kuma fahimtar al’adu daban-daban.

Haka kuma ta zama hanya ta samun kudin shiga mai kyau wanda yake taimaka mini wajen kula da wasu bukatuna na yau da kullum. Mafi muhimmanci, mutane sun fara amincewa da aikina kuma suna hadani da mutane. Wannan ita ce babbar nasara a gare ni.

Wani buri kake da shi a wannan sana’a?

Burina babba ne. Ina son in zama daya daga cikin fitattun masu daukar  hoto da bidiyo a Nijeriya da ma Afrika baki daya. Ina son aikin ya kai matakin da za a dinga jin suna na a ko’ina saboda ingancinsa.

Baya ga haka, burina shi ne in kafa cibiyar horar da matasa. Cibiyar da za ta koyar da daukar hoto, gyaran bidiyo, zane-zane da sauran fasahohin zamani. Ina son in taimaka wa matasa su dogara da kansu maimakon jiran gwamnati. wannan shi ne burina.

Kana da sakon da kake son isar wa masu karatu musamman matasa?

Sakona ga matasa shi ne su kasance masu hakuri, jajircewa da kuma neman ilimi a koda yaushe. Domin Ilimi shi ne ginshikin rayuwa. Kada su raina sana’a ko fasaha ko su kymace shi.

Kowace sana’a tana da damar canza rayuwar mutum idan an yi ta da gaskiya, da kwarewa.

Ku yi amfani da lokacinku wajen koyon abin da zai amfane ku da al’umma baki daya. Su bi mutanen da suka yi nasara a rayuwarsu suna tambayar su. Kuma ku rika addu’a. Allah zai ba ku nasara insha Allah.

Mun gode sosai

Nima na gode

Hoto
Muhammad Bakir Bello
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa
Tattaunawa

Dole Al’ummar Arewa Su Rungumi Hanyoyin Kasuwanci Na Zamani —Alfa Musa

August 28, 2026
Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina
Tattaunawa

Ba Mu Taba Biyan Kudin Fansa Ba Kuma Ba Za Mu Biya Ba – Kwamishinan Katsina

August 20, 2026
Nijeriya
Tattaunawa

2027: Shugaba Mai Gaskiya Da Hangen Nesa Nijeriya Ke Buƙata —Ahmad Shu’aibu

August 8, 2026
Next Post
Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya

Masanin Kimiyya Na Sin Ya Lashe Kyautar UNESCO-Russia Mendeleev A Fannin Tushen Kimiyya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.