Duk da yanayin rikice-rikicen kasa da kasa da sauye-sauyen manufofin cinikayya da rashin tabbas a harkokin tattalin arzikin duniya, tattalin arzikin kasar Sin ya ci gaba da nuna juriya a cikin watanni bakwai daga farkon wannan shekara. Galibin masana suna ganin cewa wannan ya faru ne saboda karfin masana’antu, da ci gaban fasaha, da fadada cinikayyar waje da kuma yadda kamfanonin Sin suka iya sauya dabaru domin fuskantar matsalolin duniya.
Bayanan hukumar kididdiga ta kasar Sin (NBS) na baya-bayan nan sun nuna cewa tattalin arzikin kasar ya samu ci gaba a rabin farko na shekarar nan, inda ma’aunin karfin tattalin arzikin kasa na GDP ya nuna an samu ci gaba da kashi 4.7 cikin dari, wanda hakan ke fayyace cewa duk da matsin lamba daga waje, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da tafiya cikin kuzari.
Na san wasu za su iya ganin hakan kamar wani siddabaru saboda bahallatsar da ke faruwa a duniya masu alaka da yakin cinikayya da sauran tashin-tashina, amma ba haka lamarin yake ba, abubuwa ne na zahiri daga dabarun karfafa tattalin arzikin kasar, ciki har da sauya tsarin masana’antun kasar daga dogaro da sarrafa kayayyaki na yau da kullum zuwa samar da kayayyaki masu amfani da fasahar zamani, kamar motocin lantarki, da mutum-mutumin inji da na’urorin makamashi mai tsafta da sauran kayayyakin fasaha wadanda ake bukata a kasuwannin duniya.
Haka kuma, ci gaban fasahar kirkirarriyar basira (AI) a kasar ya kara bude damammakin ciniki ga kamfanonin fasahar zamani na kasar Sin, musamman wajen kere-keren kayan aiki na zamani a kusan dukkan sassan rayuwa, kama daga aikin gona, tsaro, kiyaye muhalli har zuwa kayan amfani na yau da kullum.
Haka kuma, babbar kasuwar cikin gida ta kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye ci gaban tattalin arzikin kasar daga tasirin matsalolin da ke bullowa daga waje. Yawan masu amfani da kayayyaki a kasar Sin da kuma bukatun masana’antu, sun bai wa kamfanonin cikin gida har ma da na kasashen waje damar samun ci gaba. Misali a bangaren waje, kamfanin Jamus na kera kayayyakin kariya na masana’antu, watau Leser, ya zabi cibiyarsa da ke Tianjin a matsayin muhimmin wurin kirkire-kirkire da fitar da kayayyaki zuwa wasu kasuwanni. Wannan na nuna cewa kamfanonin duniya suna daukar kasar Sin a matsayin muhimmiyar kafa wajen samar da kayayyaki da kuma shiga kasuwannin Asiya har ma da sauran sassan duniya.
Haka kuma, yadda kasar Sin take da kyawawan manufofi na hadin gwiwa da cin moriya tare a tsakaninta da kasashe daban-daban na taimaka wa kasar wajen kauce wa dogaro da wata kasuwa guda.
Don haka, idan an dubi wannan ci gaba na tattalin arzikin kasar Sin a wannan lokaci na tashin-tashina a duniya, za a iya fahimtar cewa wasu daga muhimman abubuwan da suka zamo silar haka, akwai kirkire-kirkiren fasaha, da katafariyar kasuwar cikin gida da yin hadin gwiwa da sauran kasashe, kuma duka wadannan ba siddabaru ba ne. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














