Kamfanin gine-gine na kasar Sin mai suna China Railway 11th Bureau Group, ya ce ya kammala ainihin ginin sabon sashen ayyukan na’urori, tare da dukkanin kwaskwarimar ciki da wajen ginin, da kuma hasumiyar bayar da umarni ta filin jirgin saman kasa da kasa na Osvaldo Vieira dake kasar Guinea-Bissau.
Rahotanni na cewa, an tsara mika ginin bayan kammala shi ne a shekarar nan ta 2027, wanda bangare ne na aikin da zai lashe kudi har sefa biliyan 4.7, kusan dalar Amurka miliyan 8.4, wanda hukumar kare hadurran jiragen sama ta Afirka da Madagascar ta dauki nauyin gudanarwa.
Filin jirgin sama na Osvaldo Vieira dake birnin Bissau fadar mulkin kasar Guinea-Bissau, shi kadai ne filin jirgin saman kasa da kasa a kasar. An bude shi a karon farko a shekarar 1955, inda a yanzu kuma ake gudanar da wasu ayyuka na zamanantar da shi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














