Yau 17 ga wata, Sin ta fitar da “Rahoton Ci Gaban Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba (2026)”.
Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2025, adadin cinikin da Sin ta yi ya kai dala biliyan 802.251, wanda ya kai kashi 14.68% na jimillar cinikin na duniya, kuma girmansa ya zama na farko a duniya.
Kayayyaki masu amfani da makamashi na rage iska mai dumama yanayi da makamashi mai tsabta sun kai kashi 82.35% na daukacin kayayyaki maras gurbatta muhalli da kasar Sin ke fitarwa, kuma sun zama manyan muhimman nau’ikan kayayyaki irinsa 2 da Sin ke fitar zuwa ketare. (Amina Xu)
ADVERTISEMENT














